An ce CBN su biya tsofaffin ma’aikata N2.5bn bayan tsawon shekaru 10 ana gaban Alkali

An ce CBN su biya tsofaffin ma’aikata N2.5bn bayan tsawon shekaru 10 ana gaban Alkali

  • A shekarar 1996 ne aka kori wasu ma’aikata daga aiki a jami’ar ABU Zaria, sai suka shiga kotu a 2012
  • Tsofaffin ma’aikatan sun bukaci a biya su hakkokinsu da suke bin jami'ar, kuma sun yi nasara a kotu
  • Kotu ta kara ba ma’ikatan gaskiya ta ce lallai CBN su cire kudi N2.5bn, su biya wadannan mutane

Abuja - Babban kotun sauraron sabanin ma’aikata da ke zama a garin Abuja ya yi kira ga babban bankin Najeriya na CBN ya biya wasu ma’aikata hakkinsu.

Rahoton Nairametrics ya nuna Alkali Rakiya Haastrup ta bukaci bankin CBN ya biya ma’aikata 110 da aka kora daga aiki a ABU Zaria a 1996 kudin da suke bi.

Alkali mai shari’a Rakiya Haastrup ta zartar da wannan hukunci ne a ranar Alhamis da ta wuce.

Kara karanta wannan

Matan APC sun fadakar da Duniya kan shirin wasu Gwamnonin Arewa 3 na rusa Jam’iyya

Rakiya Haastrup ta shaidawa Lauyan wanda ya kawo kara cewa babu bukatar CBN ya nemi iznin babban akawun gwamnatin tarayya kafin ya biya wannan kudi.

A cewar Lauyar, shi ma akawun gwamnatin kasar yana cikin wadanda ake wannan shari’ar da su.

ABU Zaria
Jami’ar ABU Zaria Hoto: www.theabusites.com
Asali: UGC

An sabawa umarnin kotu da kwamitoci

Wadannan ma’aikata 110 sun shigar da karar ABU Zaria, akawun gwamnati na kasa da wasunsu a dalilin kin biyansu hakkokinsu kamar yadda aka bada umarni.

Kwamitoci da yawa da aka kafa sun bada shawarar a dawo da wadannan mutane aikin, a biya su kudinsu. Ganin ba ayi hakan ba ne sai aka sake komawa kotu.

Da aka koma shari’a a ranar Alhamis, lauyan da ya tsayawa wadanda ake kara, Yahaya Mohammed, ya roki Alkali ta kara masu lokaci a wannan shari’a.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

Femi Adedeji wanda yake kare ma’aikatan da suka samu nasara a kan jami’ar ya nuna bai gamsu da rokon Mohammed ba, ya zarge shi da kokarin ci masu lokaci.

Ku biya su N2.5bn

A karshe, kotu ta bukaci jami’ar ABU Zaria da ke jihar Kaduna ta biya wadannan kudi har N2.5bn daga cikin kudin hakkokinsa da gwamnati ta rika aikowa jami’ar.

Da aka yi hukunci a 2015, lauyoyin ma’aikatan sun doke wadanda suka kare jami’ar. Hakan ta sa aka daukaka karar zuwa NIC, a nan ma aka ba ma’aikatan gaskiya.

Gyara dokoki da tsarin mulki

Rahotanni sun zo cewa ana so a karo kujeru 219 da za a ware domin mata a Majalisun wakilan tarayya da na dattawa da kuma na dokoki duk jihohin kasar nan.

Kwamitin gyara kundin tsarin mulki ya kuma bada shawarar a rika bada katin zama 'dan kasa ga duk mutumin da ya zo daga kasar waje, ya auri wata 'yar Najeriya.

Kara karanta wannan

Kotu ta yankewa wasu masu walder 4 daurin shekaru 7 a kurkuku saboda satar N15m

Asali: Legit.ng

Online view pixel