Ana so a karo kujeru 219 da za a ware domin mata zalla a Majalisun tarayya da dokoki

Ana so a karo kujeru 219 da za a ware domin mata zalla a Majalisun tarayya da dokoki

  • Kwamitin majalisa da ke aiki a kan yi wa tsarin mulki kwaskwarima ya amince a kan kara kujeru
  • An kawo shawarar kara adadin kujeru a majalisa ta yadda za a samu karin mata da ke wakiltar jama’a
  • Wannan kwamiti ya yarda ayi wa dokar kasa garambuwal kan wanda za a ba katin zama ‘dan Najeriya

Abuja - ‘Yan kwamitin majalisar wakilan tarayya na gyara kundin tsarin mulki sun amince da maganar kirkiro wasu karin kujeru 219 da za a warewa mata.

Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 26 ga watan Junairu 2022 cewa kan kwamitn ya hadu a kan a ware kujeru 111 saboda mata a majalisar tarayya.

Honarabul Nkeiruka Onyejeocha (APC, Abia) da wasu ‘yan majalisa 119 suka kawo wannan kudiri, suna neman a gyara wasu sassa a cikin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta soke sababbin gyare-gyaren da Majalisa tayi a kasafin kudin 2022

Kudirin zai yi wa sassa na 48, 49, 71, 77, 91 da 117 na kudin tsarin mulkin kasa garambawul, ta yadda za a kara adadin kujerun majalisa a Abuja da duka jihohi.

Idan kudirin ya samu shiga, za a samu karin kujerar Sanata daya a kowace jiha da za a bar wa mata, da kuma kujeru biyu daga kowace jiha a majalisar wakilai.

Hakan ya na nufin za a samu karin kujeru 108 na mata zalla a majalisar dokoki 36 na jihohin Najeriya. Mafi yawan matan da ke majalisa ba su nan da ake zaman.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan Majalisa
Zaman kwamitin majalisar wakilan tarayya Hoto: @HouseNGR/Facebook
Asali: Facebook

Bayan wannan magana ta karbu wajen jama’a da aka yi zama a zauren majalisa a ranar Talata, kwamitin zai kai kudirin gaban majalisa domin ayi muhawara.

A ba mata 35% na mukamai

Jaridar ta ce kwamitin ‘yan majalisar sun yi fatali da wani kudiri da aka kawo da zai wajabta warewa mata akalli 35% na duk wasu mukamai da za a raba a kasa.

Kara karanta wannan

Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40

An yi watsi da wannan kudiri bayan ya samu suka daga wasu ‘yan kwamitin. Uzoma Abonta yace sai dai mata su zaba ko a ba su 35% na mukamai ko karin kujeru.

Honarabul Uzoma Abonta yana ganin ya kamata a bar maganar kashi 35% ya zama tsarin jam’iyya.

Katin 'dan kasa ga wanda ya auri 'Yar Najeriya

Har ila yau, mata sun yi nasara a makon nan inda kwamitin majalisa ya amince a rika bada katin zama ‘dan kasa ga duk mutumin kasar waje da ya auri ‘yar Najeriya.

Joy Ezeilo ta samu kwamitin ya yarda ayi wa sashe na 26 (2a) na kundin tsarin mulkin 1999 garambuwal. Yanzu za a tafka muhawara kan wannan a zauren majalisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel