Matan APC sun fadakar da Duniya kan shirin wasu Gwamnonin Arewa 3 na rusa Jam’iyya

Matan APC sun fadakar da Duniya kan shirin wasu Gwamnonin Arewa 3 na rusa Jam’iyya

  • Wasu mata a karkashin lemar 'Coalition of Progressive Women in Nigeria' su na so daga zaben APC
  • Kungiyar CPWN ta ce matsalar da za a samu wajen zaben shugabannin APC zai iya kawo cikas a 2023
  • Wannan kungiya ta na zargin wasu gwamnoni da shirin kawowa APC matsala a gangamin da za ayi

Abuja - Wata kungiya mai suna Coalition of Progressive Women in Nigeria (CPWN) ta ba jam’iyyar APC shawarar da dakatar da zaben shugabanninta na kasa.

A wajen wani taro da wannan kungiya ta mata masu son cigaba suka yi a garin Abuja, sun bukaci a fasa zaben shugabanni saboda makarkashiyar wasu gwamnoni.

Legit.ng ta samu halartar wannan taro a ranar Talata 25 ga watan Junairu 2022 inda shugabar CPWN, Cecilia Ikechukwu ta ce dage zaben shi ne alheri ga APC.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta shiga matsi, gwamnonin kudu 3 sun ce ba ruwansu da takarar Atiku

Misis Cecilia Ikechukwu ta na ganin cewa janye zaben daga watan Fubrairu zai taimakawa ‘ya ‘yan jam’iyya su gabatar da korafin da suke da shi domin ayi gyara.

Jaridar Vanguard ta rahoto Ikechukwu ta na kira ga kwamitin rikon kwarya su yi kokarin dinke barakar da ta shigo cikin jam’iyyar a maimakon zaben shugabanni.

Matan APC
Coalition of Progressive Women in Nigeria Hoto: Charles Anya
Asali: UGC

A ja-kunnen Gwamnoni 3

A jawabin da ta gabatar, Ikechukwu ta fadakar da jama’a a game da katsalandan da wasu gwamnoni suke yi wa jam’iyya su na son ransu a madadin cigaban APC.

Gar-da-gar wannan Baiwar Allah tayi kira ga majalisar koli ta APC da ta ja kunnen gwamnoni uku.

Wadannan gwamnoni su ne Mai girma Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da kuma Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Kebbi.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

Kungiyar CPWN ta yi gargadi cewa idan aka dage a kan sai an yi zaben shugabannin na kasa a watan na gobe, mata a gida da wajen kasar nan za su nuna karfinsu.

A karshe CPWN ta roki Mai girma Muhammadu Buhari, sauran gwamnonin APC da jagororin jam’iyya su tashi-tsaye wajen ceto APC daga gwamnonin nan uku.

Ekiti 2022

A jiya da yamma aka ji 'ya ‘yan jam’iyyar PDP sun fito da ‘dan takarar gwamna a zaben gwamnan jihar Ekiti da za ayi a bana. Yanzu haka ana sauran 'dan takarar APC.

‘Dan takarar da Ayo Fayose ya tsaida, Bisi Kolawole ne ya yi nasara, zai rike tutar jam'iyyar PDP bayan ya doke Segun Oni, Biodun Olujumi da wasu masu neman takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel