Hukumar aikin yan sanda PSC ta ce a sake sabon bincike kan Abba Kyari

Hukumar aikin yan sanda PSC ta ce a sake sabon bincike kan Abba Kyari

  • An umurci Sifeto Janar na yan sanda ya kaddamar da sabon bincike kan alakar Abba Kyari da dan damfara Hushpuppi
  • Hukumar aikin yan sanda PSC ta umurci IGP Alkali bisa shawaran da ta samu daga wajen Antoni Janar na kasa, Abubakar Malami
  • Wannan ya biyo bayan binciken da aka gudanar watanni bayan da hukuncin da akayi shirin yi masa

Hukumar aikin yan sanda (PSC) ta umurci Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya kaddamar da sabon bincike kan alakar dake tsakanin dakataccen jami'i Abba Kyari, da dan damfara, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

A cewar Sahara Reporters, wannan umurni ya biyo bayan shawarar da Antoni Janar na kasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya bada.

Rahoton yace a ranar Laraba, 26 ga Junairu, Antoni Janar yace hujjojin dake cikin takardan binciken da aka gudanar basu da karfin da za'a kama Abba Kyari da laifi a kotu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan Hanifa, an sake kashe wata yarinya a jihar Kano: Gwamna Ganduje

Abba Kyari
Hukumar aikin yan sanda PSC ta ce a sake sabon bincike kan Abba Kyari
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ruwaito Malami na cewa binciken da IGP ya gudanar kan Abba Kyari bai da karfi sosai kuma ana bukatan karin bayanai daga bakinsa.

Wannan babban jami'i yace:

"Shawarar Antoni Janar itace akwai bukatar a zurfafa bincike; saboda hujjojin da aka gabatar kan Abba Kyari basu da karfin kamashi da laifi duk da cewa an tabbatar da lallai ya aikata laifi. Amma hujjojin dake kasa basu da karfin kamashi a kotu."

Abba kyari ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa

An samu bayanai akan yadda Kyari ya amsa tambayoyi akan zarginsa da damfarar dala miliyan 1.1 da wani fitaccen dan Instagram, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.

FBI ta zargi yadda Hushpuppi ya hada kai da Kyari wurin kama wani abokin harkarsa, Chibuzo Vincent, don barazanar fallasa damfarar dala miliyan 1.1 da ya yi ga wani dan kasuwar Qatar.

Kara karanta wannan

Kotu ta zabi ranar Valentine don yanke wa Hushpuppi hukunci a Amurka

FBI ta Amurka ta ce Hushpuppi ya tura dala 20,600 cikin asusun bankin Kyari.

Sakamakon haka ne PSC ta dakatar da Kyari sannan ta samar da kwamiti na musamman don bincike (SIP) akan gano ko Kyari ya na da hannu a damfarar.

IGP ya mika rahoton binciken Abba Kyari da Hushpuppi gaban PSC

A ranar 20 ga Disamba 2021, Sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Alkali Usman, ya gabatar da takardun rahotanni gaban hukumar ‘yan sanda dangane da Abba Kyari .

The Nation ta bayyana yadda wani jami’in PSC, Braimoh Adogame Austin, a ranar Lahadi, 19 ga watan Disamba ya ce hukumar za ta zauna ta tattauna akan rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel