PDP na fuskantar barazanar ficewar dinbin mabiya kan batun tsaida ‘Dan takaran 2023

PDP na fuskantar barazanar ficewar dinbin mabiya kan batun tsaida ‘Dan takaran 2023

  • Kungiyar Vanguard for Justice ta gargadi PDP a kan yin kuskuren ba ‘Dan Arewa takara a 2023
  • Vanguard for Justice ta ce jama’a da-dama za su yi watsi da jam’iyyar hamayyar idan suka yi hakan
  • Shugaban tafiyar, Emmanuel Nduka ya ce adalci shi ne PDP ta ba ‘Dan Kudu tuta a zaben na 2023

Abuja - Muddin jam’iyyar PDP ta ba mutumin Arewa tikitin takarar shugaban kasa a 2023, Vanguard for Justice ta ce mabiyanta za su fice daga cikinta.

Jaridar Vanguard ta rahoto kungiyar ta Vanguard for Justice ta na cewa jam’iyyar PDP ya na kokarin sake kai takararta zuwa yankin Arewa a zaben 2023.

Shugaban kungiyar Vanguard for Justice na kasa watau Mista Emmanuel Nduka ya na ganin idan hakan ta faru, manyan ‘yan siyasar Kudu za su sauya-sheka.

Kara karanta wannan

Baki ya ke yanka wuya: An bukaci Tinubu ya bada hakurin abubuwan da ya fada tun 1997

Emmanuel Nduka ya ce adalci da zaman lafiya da tafiya da juna shi ne jam’iyyar PDP ta damka tutar takarar shugaban kasa ga ‘dan siyasar Kudu a zaben badi.

Haka zalika wannan kungiya ta ce abin da jama’a su ke bukata shi ne ‘Dan kudu ya karbi mulki.

PDP a taro
Gwamnonin PDP a taro Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Adalci shi ne a ba Kudu takara

“Mika mulki ga Kudu zai farfado da hadin-kan ‘Yan Najeriya, ya kawo adalci da zaman lafiya. Mafi yawan masu cewa mulki ya tafi Kudu, ‘Yan Arewa ne.”
“A wannan gaba akwai dattijon Arewa, Tanko Yakasai wanda kwanan nan ya fito yana cewa rashin adalci ne ‘Yan Arewa su yi takarar shugaban kasa.”
“Ya za ayi a ce ‘Yan yankin Arewa kawai suke ta yin mulki? Babu adalci a wannan lamarin.”

Kara karanta wannan

Zaben APC: ‘Yan Jam’iyya a Arewa sun tsaida ‘Dan amanar Buhari a matsayin ‘dan takararsu

“Idan wa’adin Muhammadu Buhari ya cika, sai Arewa ta hakura. Buhari ya yi takwas, a kan me wani ‘Dan Arewa zai nemi takara, ya yi shekaru takwas?”

A jawabin da ya fitar, Nduka ya gargadi gwamnonin kudu maso kudu da suke harin tsayawa takara a matsayin matakin shugaban kasa tare da wani ‘Dan Arewa.

New Telegraph ta rahoto shi yana cewa idan PDP ta tafi a haka, za ta yi mamakin abin da zai faru da ita, domin watakila karshen ta ya zo kenan a tarihin siyasa har abada.

Tinubu ya jawowa kan sa

A makon nan ne aka ji wasu ‘ya ‘ya da shugabannin jam’iyyar APC a yankin Arewa sun yi kira ga Asiwaju Bola Tinubu ya nemi afuwa kan kalaman da ya yi a baya.

Kungiyar ta APC ta bukaci Bola Tinubu ya lashe amansa kan wasu kalaman da ya yi a shekarar 1997 a lokacin Marigayi Janar Sani Abacha ya na tsakar mulkin soja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel