Shugaba Buhari zai miƙa mulki ga ɗan takarar APC a 2023 Insha Allahu, Garba Shehu ya magantu

Shugaba Buhari zai miƙa mulki ga ɗan takarar APC a 2023 Insha Allahu, Garba Shehu ya magantu

  • Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya jaddada fatansa cewa Buhari zai miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin APC a 2023
  • Shehu ya faɗi haka ne yayin da yake martani kan zargin cewa Buhari ya ɗana wa gwamnatin gaba tarko guda biyu da zai iya nuna gazawarta
  • Ministan kudi, Hajiya Zainab Ahmed, ta ce a sanin ta Buhari na kan mulki har watan Disamba mai zuwa

Abuja - Babban mai taimaka wa shugaban ƙasa ta bangaren yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyana yaƙininsa cewa jam'iyyar APC ce zata sake kafa gwamnati a 2023.

Shehu ya jaddada fatansa cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari zai miƙa mulki ne ga sabuwar gwamnatin APC, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa a Najeriya

Ya yi wannan furucin ne a takaice yayin da yake zantawa da manema labarai, jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa na ranar Laraba.

Garba Shehu
Shugaba Buhari zai miƙa mulki ga ɗan takarar APC a 2023 Insha Allahu, Garba Shehu ya magantu Hoto: stalliontimes.com
Asali: UGC

Shehu, ya faɗi haka ne yayin da yake martani kan tambayar cewa shugaba Buhari ya ɗana tarko ga gwamnatin gaba game da lamarin cire tallafin man fetur.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan wannan, gwamnatin Buhari ta nemi a ɗage aiwatar da kudirin kafa sabuwar ma'aikatar albarkatun man fetur, (PIA) zuwa watanni 18 masu zuwa, wanda aka tsara fara ta a watan Fabrairu.

Hadimin shugaban ƙasan, wanda aka gaya wa cewa matakan na nuna alamar an ɗana wa gwamnatin gaba tarko da zai nuna gazawarta, yace:

"Amma ita (Ministan kuɗi, kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Hajiya Zainab Ahmed) ta baku amsar nan."
"Da farko, ina son ku gane cewa shugaba Buhari a shirye yake kuma muna fatan mu miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin APC, Insha Allahu."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanata ya sanar da kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a 2023

Me ministan kuɗi tace yayin amsa wannan tambaya?

Da take amsa tambayar, ministan kuɗi, kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed, ta ce ta san cewa shugaban Buhari ne a kan mulki har zuwa watan Disamba.

"Na san cewa shugaban ƙasa Buhari, shi ne a kan mulkin shugabamcin Najeriya har zuwa watan Disamba."

A wani labarin na daban kuma Kungiyoyin mata sama da 600 sun mamaye titunan Abuja, sun goyi bayan gwamna ya gaji Buhari a 2023

Kungiyoyin mata daban-daban sama da 600 sun gudanar da tattaki domin nuna goyon bayan su ga takarar gwamna Yahaya Bello a 2023.

Matan sun bayyana cewa Bello ya cancanci ya ɗora daga inda Buhari ya tsaya kuma yana tafiya da mata a mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel