Da Dumi-Dumi: Sanatan APC ya sanar da kudirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Da Dumi-Dumi: Sanatan APC ya sanar da kudirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Sanata a jam'iyyar APC, Sanata Rochas Okorocha, ya sanar da majalisar dattawa kudirinsa na neman ɗarewa kujerar shugaban ƙasa a 2023
  • Tsohon gwamnan jihar Imo, a wata wasika da ya tura wa shugaban majalisa, yace zai gudanar da taron manema labarai na duniya kan manufarsa
  • Ya ce yan Najeriya na bukatar nagartaccen shugaba da zai iya shawo kan matsalolin da suka addabi ƙasa

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Punch ta rahoto cewa Okorocha ya bayyana haka ne a wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta a zaman yau Laraba.

A ranar Litinin, 31 ga watan Janairu, 2022, tsohon gwamnan zai yi jawabi a wurin taron manema labarai na duniya, inda ake sa ran zai yi ƙarin haske kan manufofinsa.

Kara karanta wannan

Najeriya ce ta 1 cikin jerin kasashen Afrika da ake amfani da man Bilicin, Sabon Bincike

Sanata Rochas Okorocha
Da Dumi-Dumi: Sanatan APC ya sanar da kudirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A wasikar, The Nation ta rahoto Sanata Okorocha yace:

"Kamar yadda kuka sani, hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta fitar da jadawalin zaɓen 2023, wanda ya haɗa da na ofishin shugaban tarayyan Nigeria."
"Yayin da zaɓen ke kara matsowa kullum kwana, yan Najeriya sun damu kan mutumin da zai rike musu amanar ƙasa. Wanda zai iya magance musu abin da ya hana su bacci."

Nagartar da ake bukatar shugaba na gaba ya tattara

Tsohon gwamnan ya zayyano wasu nagarta da yan Najeriya ke son wanda zai jagorance su a zabe na gaba ya tattara su, wanda ya haɗa da;

"Ɗan Najeriyan da ba ruwan shi da banbancin kabila, wanda zai iya haɗa kan ƙasa wuri ɗaya. Mutumin da yake da zuciyar tausayi da zai kula da talakawa, da masu rauni."

Kara karanta wannan

Ado Doguwa ya samu karuwar 'diya na 28, ya lashi takobin haifan 30 kafin 2023

"Shugaban da zai iya samar da hanyoyin arziki ga yan ƙasa, ta hanyar warware matsalolin talauci, rashin tsaro da zaman kashe wandon matasa."
"Sakamakon haka zan kira gagarumin taron manema labarai na duniya kan kudirina na neman ofishin shugaban ƙasa a Najeriya. Ina rokon addu'o'in ku da fatan alkairi."

A wani labarin na daban kuma Pantami ya faɗi babban abinda yan bindiga ke amfani da shi wajen ayyukan ta'addanci a Arewa

Minsitan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, yace yan bindiga na ribatar yawan faɗin kasa a jihohin arewa maso gabas wajen aikata ta'addanci.

Sheikh Pantami yace hudu daga cikin jihohin Najeriya shida da suka fi faɗi duk suna yankin arewa maso gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel