Buhari zai sake aika wa Sanatoci da sunan Hadimarsa da aka ki amincewa a ba ta mukami

Buhari zai sake aika wa Sanatoci da sunan Hadimarsa da aka ki amincewa a ba ta mukami

  • Shugaban kasa ya bukaci a tantance Lauretta Onochie a majalisar dattawa
  • Sanatoci sun ki yarda a ba Lauretta Onochie mukamin kwamishina a INEC
  • Majiya ta ce har yanzu shugaba Muhammadu Buhari bai janye sunanta ba

Duk da majalisar dattawa ta yi fatali da rokon shugaban kasa na nada Lauretta Onochie a matsayin kwamishinar INEC, watakila a sake aika sunanta.

Punch ta fitar da rahoto a ranar Talata, 13 ga watan Yuli, 2021, ta ce wata majiya dafa fadar shugaban kasa ta shaida mata za a kuma tura sunan Onochie.

Majiyar ta ce har gobe shugaban kasa bai fitar da rai cewa Misis Onochie za ta hau kujerar babbar kwamishina na hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ba.

KU KARANTA: Kungiyar Ibo ta soki Bello a kan takarar 2023

Jaridar ta ce har zuwa yanzu, shugaba Muhammadu Buhari bai janye sunan hadimar ta sa daga majalisar tarayya ba, hakan ya nuna sam bai karaya da ita ba.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: Bayan dogon cece-kuce, majalisa ta karbi rohoton gyara dokar zabe

“Ganin cewa har yanzu mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari — wanda ya bada sunanta bai janye ba, ya nuna ya yarda da tsarin da ake bi.”
“Sannan ya yarda cewa za a iya tantance Onochie (Lauretta). Har yanzu ya yarda da ita.”

KU KARANTA: Bai kamata Sanatoci su tantance Lauretta Onochie ba - Jega

Buhari zai sake aika wa Majalisa da Hadimarsa da aka ki amincewa a ba ta mukami
Shugaban majalisa, Ahmad Lawan Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Zuwa yanzu fadar shugaban kasa ba ta ce komai ba a kan matakin da gwamnati ta dauka.

Jaridar ta tuntubi Mallam Garba Shehu domin jin ta bakinsa, amma ba ta yi nasara ba. Bai amsa kiran da aka yi masa a waya ba, sannan bai tanka sakonni ba.

Hujjar da kwamitin da ya zauna da wannan mata ya bada shi ne nada ta a kujerar kwamishina zai ci karo da tsarin FCC da ta ce a ba kowace jiha dama iri daya.

Kafin a sake kai wa majalisar dattawan kasar sunan Onochie, ya kamata kwamishina mai-ci a yanzu da ta fito daga jihar Delta ta yi murabus, ta ba hadimar dama.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

Kwamitin majalisa ya yi daidai - Ahmed Musa Husseini

Masana irinsu Ahmed Musa Husseini sun yi farin ciki da majalisar dattawa ta ki amince wa da Onnochie, ya ce ta yi kusa da yawa da shugaban kasa da APC.

A cewar Husseini, zaben ta a kujerar INEC, tamkar gwamnatin Goodluck Jonathan ta nada Reno Omokri ko femi Fani-Kayode a matsayin kwamishinan zabe.

An san ana zargin cewa mai ba shugaban kasar shawara, ‘yar jam’iyya APC ce. Tuni dai wannan mata ta karyata wannan zargi, amma dai akwai alamun tambaya.

Zaben Lauretta Onochie a matsayin shugaba a hukumar INEC da ya kamata a ce ta na cin gashin kanta ya jawo sukar PDP, ana ganin Onnochie ba za ta iya adalci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel