Bidiyo: Diyar biloniya Dangote, Halima Dangote ta gigita masu kallo da salon rawanta

Bidiyo: Diyar biloniya Dangote, Halima Dangote ta gigita masu kallo da salon rawanta

- Halima, diyar hamshakin mai arzikin Afrika, Aliko Dangote, ta sanya masoya cikin shauki mai yawan gaske

- Bayan Halima taje wani taro, ta burge jama'a da wani salon rawarta mai kayatarwa da rikitarwa

- Bidiyon rawar da tayi ya karade kafafen sada zumuntar zamani yayin da jama'a suka yi ta tsokaci

Diyar attajirin dan kasuwar nan, Aliko Dangote, Halima, ta zamanto abar labari a kafafen sada zumuntar zamani domin ta burge jama'a kwarai.

Matar mai karancin shekaru wacce kowa ya sani da matukar tsantseni da kamun kai ta bayyana tana kwasar rawa mai daukar hankali a wani taro da ta je.

Ba kamar yadda ake zato ba, cikin kwarewa Halima ta bayyana a fili tana rawa tare da bin wakar wani mawaki sanannen mai suna Teni, cike da shauki.

KU KARANTA: Gabatowar watan Ramadan: Mabiya Abduljabbar sun roki Ganduje ya bude masallacinsu

Bidiyo: Diyar biloniya Aliko Dangote, Halima Dangote ta gigita masu kallo da salon rawanta
Bidiyo: Diyar biloniya Aliko Dangote, Halima Dangote ta gigita masu kallo da salon rawanta. Hoto daga @Hausaroom
Asali: Instagram

KU KARANTA: Ko ɗan da na haifa aka sace ba zan biya kudin fansa ba, zan yi addu'ar shigarsa aljanna, El-Rufai

Ko kadan ba a hango tsoro ko shakka tattare da Halima ba domin cikin kwarewa ta kwashi rawar. Take a nan masoya cike da shauki da begenta suka yi ta yada bidiyon Halima Dangote tana rawar wacce ta tafi da tunaninsu har da damansu suke tsokaci iri-iri akai.

Wata High_class_sokoto_kayan_mata tace: "Gata da salo, (ta yi rawarta a natse kuma cike da kwarewa)."

Hafsin _fashion kuwa cewa tayi: "Ba zan iya kirga sau nawa na kalli wannan bidiyon ba."

Khadeejjarh tace "Masu arziki basa wahalar da kansu a rawa."

Sameerahs_closet ta ce: "Tabbas ta kware a rawa".

A wani labari na daban, Abdulrahman Dambazau, tsohon shugaban sojin kasa, ya kamanta kungiyoyin IPOB da OPC da kungiyar Boko Haram.

A cewarsa OPC da IPOB suna yunkurin tayar da tarzomar kabilanci a Najeriya. Ya yi wannan bayanin ne a ranar Juma'a a Abuja, inda Dambazau ya bayyana kamanceceniyarsu da Boko Haram wacce ta fara a 2009.

Ya yi bayani akan yadda suke nuna zakewa da kuma kawo cikas.

"Ba jihohi suke yi wa yaki ba: suna da wata manufar ta daban ta raba kan al'ummar kasar Najeriya. Basu yarda da hadin kai ba kamar yadda Boko Haram take," a cewar Dambazau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel