Shehu Sani: Messi da Salah na burge matata, amma da nace yan wasa mata na burge ni sai murtuke fuska

Shehu Sani: Messi da Salah na burge matata, amma da nace yan wasa mata na burge ni sai murtuke fuska

  • Shehu Sani ya bayyana cewar Lionel Messi da Mohammed Salah suna burge matarsa idan suna taka leda
  • Tsohon sanatan ya bayyana cewa hakan ya samu karbuwa amma a duk lokacin da ya ambaci wacce ta fi burge shi a yan wasan Super Falcons sai shiru ya biyo baya a gidan
  • Sani a wata wallafa da ya yi a Twitter a ranar Talata, 25 ga watan Janairu, ya bayyana cewa ba a yiwa maza adalci

Sanata Shehu Sani ya bayyana diramar da ake yi a gidansa a kan kwallon kafa da kuma yan wasan da kowa ya fi so tsakaninsa da matarsa.

A wata wallafa da ya yi a shafin Twitter a ranar Talata, 25 ga watan Janairu, tsohon sanatan daga Kaduna ya bayyana cewar matarsa na son ganin Lionel Messi da Mo Salah suna taka leda a kungiyar kwallon kafa daban-daban.

Kara karanta wannan

Ahmed Musa ya wallafa sako mai ratsa zuciya bayan fitar Najeriya daga AFCON

Shehu Sani: Messi da Salah na burge matata, amma da nace yan wasa mata na burge ni sai murtuke fuska
Shehu Sani: Messi da Salah na burge matata, amma da nace yan wasa mata na burge ni sai murtuke fuska
Asali: UGC

Sai dai ya ce yanayinta kan sauya a duk lokacin da ya bayyana wacce ta fi burge shi a cikin yan wasan Super Falcons wato yan wasa mata.

Kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Uwargidata ta ce tana son Messi da Salah a duk lokacin da suke buga wasa kuma na yi na'am da hakan; a ranar da na ambaci yan wasa mata biyu da suka fi burge ni a tawagar kasarmu, sai shiru ya biyo baya a falon. Ina adalci a nan idan shi namiji ba zai iya so ba?

Shehu Sani ya bayyana wani sirri mai ban dariya game da matarsa da diyarsa

A gefe guda, mun kawo a baya cewa tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya bayyana cewa a kodayaushe diyarsa kan dakile kokarin matarsa na ganin ta damki wayarsa.

Sanatan mara shayin magana wanda ya sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta People Democratic Party (PDP) a kwanan nan ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Ustazai: Wankan kamala na amarya da ango a wajen liyafar aurensu ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta

Ya rubuta:

“A duk lokacin da na bai wa diyata wayata domin ta buga wasanni da shi, sai na lura cewa mahaifiyaryta ta kan so kiranta zuwa kicin; diyar tawa mai wayo sai ta mika mani wayar kafin ta tafi kicin din; toh daga nan sai ka ga mahaifiyar tana bata rai. Ina son diyata.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel