Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC na neman tsohon dan majalisar tarayya ruwa a jallo don abin da ya wallafa a Facebook

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC na neman tsohon dan majalisar tarayya ruwa a jallo don abin da ya wallafa a Facebook

  • Dave Umahi, Gwamnan Jihar Ebonyi, ya ayyana neman tsohon dan majalisa, Hon Linus Okorie ruwa a jallo bisa rubutu da ya yi a Facebook
  • Gwamnan ya sanar da hakan ne ta bakin kwamishinan labarai da shari'a na jihar bayan taron majalisar kolin tsaro na jihar inda ake zarginsa da tunzura mutanen da suka kashe jami'an Ebubeagu
  • A bangarensa, tsohon dan majalisar Linue Okorie ya yi ikirarin cewa Gwamna Umahi kawai yana son ya rufe wa yan adawa baki a jihar ne shi yasa ya ke masa bita da kulli

Ebonyi - Gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi ya ayyana neman tsohon Dan Majalisar Wakilai na Tarayya, Hon, Linus Okorie, ruwa a jallo kan wallafa rubutu da ka iya tunzura mutane a jihar a Facebook, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ba zan yi jinkiri wajen rattafa hannu kan hukuncin kisa kan makashin Hanifa Abubakar ba, Ganduje

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC ya ayyana neman tsohon dan majalisa ruwa a jallo don abin da ya wallafa a Facebook
Gwamnan Ebonyi ya ayyana neman tsohon dan majalisa ruwa a jallo don abin da ya wallafa a Facebook. Hoto: Vangaurd NG
Asali: UGC

Linus Okorie ya wakilci mazabun Ohaozara/Onicha/Ivo a majalisar dokoki na tarayya daga 2011 zuwa 2019.

Gwamnatin ta yi ikirarin cewa rubutun da dan majalisar ya yi ne ya janyo aka halaka wani jami'in tsaro na Ebubeagu a karamar hukumar Ikwo na jihar ta Ebonyi.

Wannan sanarwa ta kunshe ne cikin sako da kwamishinan watsa labarai da wayar da kan mutane, Barista Orji Uchenna da kwamishinan Sharia kuma Antoni Janar na jihae, Barista Cletus Afoke suka fitar.

Sanarwar ta ce an dauki matakin ne bayan taron majalisar koli na tsaro a jihar.

Mr Orji ya ce:

"Majalisar kolin tsaro na jihar ta duba abubuwan da ke cikin rahoton don haka ta ayyana neman Hon Linus OKorie ruwa a jallo saboda wallafa maganganu da masu iya tunzuru mutane a Facebook, an gano wasu daga cikin maganganun ne suka tunzura rikicin da ya janyo datse han jami'in Ebubeagu."

Kara karanta wannan

Da duminsa: FG ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur har sai baba ta gani

Mr Orji ya kuma ce akwai wasu mutanen da ake zargin suna da hannu wurin wannan mummunan kisar gillar.

Ya ce majalisar kolin ta yi kira ga jami'an tsaro su gaggauta bincike a kan lamarin da nufin zartar da hukunci kan wadanda aka samu da laifi.

Gwamna Umahi ne ya jagoranci zaman majalisar tsaron da ta samu hallarcin shugabannin hukumomin tsaro a jihar.

Martanin tsohon dan majalisa, Linus Okorie

A bangarensa, tsohon dan majalisar Hon Okorie ya ce ayyana neman sa ruwa a jallo wani sharri ne da Umahi ya ke kitsa wa don musgunawa yan adawa a jihar Ebonyi.

Ya ce gwamnatin jihar tana shirin amfani da Ebubeagu domin halaka shi da sunan ana son kama shi.

Ya kuma yi ikirarin cewa gwamnatin jihar na kokorin rufe wani cibiyar yin bukukuwa mallakarsa a Abakaliki.

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kwara ta haramta bara a jihar, ta yi yarjejeniyar da al'ummar Hausawar Ilori

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel