Da Dumi-Dumi: Tsohuwar Sakataren gwamnati, Gimbiya Adenrele, ta riga mu gidan gaskiya

Da Dumi-Dumi: Tsohuwar Sakataren gwamnati, Gimbiya Adenrele, ta riga mu gidan gaskiya

  • Tsohuwar sakatariyar gwamnatin jihar Legas, Gimbiya Adenrele Adeniran-Ogunsanya, ta riga mu gidan gaskiya
  • Rahoto ya nuna cewa babu wani cikakken bayani kan musabbabin mutuwarta amma an bayyana cewa ta cika ne bayan fama da rashin lafiya
  • Kafin rasuwarta, ta yi aiki a matsayin SSG a tsakanin 2007 zuwa 2011, lokacin ministan Ayyuka da gidaje Babajide Fashola, yana gwamna

Lagos - Tsohuwar sakatariyar gwamnatin jihar Legas, Gimbiya Adenrele Adeniran-Ogunsanya, ta rigamu gidan gaskiya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Marigayya Adenrele ta mutu ne ranar Talata, ta na da shekaru 74 a duniya.

Adeniran-Ogunsanya, ta yi aiki a matsayin sakateriyar gwamnatin jihar Legas tsakanin 2007-2011, lokacin Babatunde Raji Fashola, ministan ayyuka da gidaje na yanzu, yake matsayin gwamna.

Adenrele Adeniran-Ogunsanya
Da Dumi-Dumi: Tsohuwar Sakataren gwamnati, Gimbiya Adenrele, ta riga mu gidan gaskiya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Duk da babu wasu cikakkun bayanai kan musabbabin mutuwar ta, amma an bayyana cewa ra rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Mahaifiyar Ɗan Majalisa a Kano da Yan Bindiga Suka Sace Ta Kubuta Bayan Biyan Miliyan N40m

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Marigayyar ɗiya ce ga Adeniran Ogunsanya, fitaccen ɗan siyasa a Najeriya ɗan asalin garin Ikorodu kuma aboki na kusa ga marigayi Nnamdi Azikwe.

Kazalika, kafin mutuwarta ta kasance a ɓangaren Injiniya Funsho Williams, ɗan takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar PDP, wanda aka yi wa kisan gilla a jihar Legas.

Daga baya ta sauya sheƙa zuwa jam'iyyar (AC) inda aka naɗa ta sakatariyar gwamnatin jihar karkashin mulkin Fashola.

Mahaifiyar Ɗan Majalisa a Kano da Yan Bindiga Suka Sace Ta Kubuta Bayan Biyan Miliyan N40m

A wani labarin na daban kuma yan bindigan da suka sace mahaifiyar kakakin majalisar dokokin jihar Kano sun sako ta bayan sun karɓi kudin fansa

Bayan shafe kwanaki 13 a hannun yan bindiga, mahaifiyar ɗan majaisar jihar Kano da aka yi garkuwa da ita, Hajiya Zainab, ta shaƙi iskar yanci

Kara karanta wannan

Dubun wani matashin saurayi da ake zargi da kashe budurwarsa ya cika

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Hajiya Zainab, ta kuɓuta ne ranar Talata, bayan biyan masu garkuwa da mutane zunzurutun kuɗi miliyan N40m a matsayin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel