Bidiyon dan sanda ya na cin zarafin wata mata, ya na barazanar harbe ta

Bidiyon dan sanda ya na cin zarafin wata mata, ya na barazanar harbe ta

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun ce sun kama wani dan sanda wanda ya ci zarafin wata mata a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta
  • A wani bidiyo wanda aka dinga wallafawa a ranar Juma’a, an ga wani dan sanda ya na rike da bindiga ya na harbawa sama don tsoratar da matar
  • An ji mutumin da ke daukar bidiyon ya na jan kunnen dan sandan sannan ya bukaci sauran jami’an tsaro a kan su dauki mataki a kan abinda abokin aikin su ya yi

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta kama dan sanda da ya ci zarafin wata mata a wani bidiyo wanda ya yadu a kafafen sada zumunta.

A bidiyon, wanda ya yi yawa a ranar Juma’a, an ga wani dan sanda rike da bindiga ya na cin zarafin wata mata yayin da yake harbi don ya tsoratar da ita, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ka rike girman ka: Tsohon Minista ya ja-kunnen Shugaba Jonathan a kan kwadayin mulki

Bidiyon dan sanda ya na cin zarafin wata mata, ya na barazanar harbe ta
Bidiyon dan sanda ya na cin zarafin wata mata, ya na barazanar harbe ta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
“Kina hauka ne, ni tsaran ki ne, sai na kashe ki,” kamar yadda aka ji dan sandan ya na fadi da turanci yayin da ya ke kokarin marin matar.

TheCable ta ruwaito cewa, wani mutum wanda ba ya cikin bidiyon ya ja kunnen dan sandan akan cin zarafin matar yayin da ya hori sauran ‘yan sanda da kada su kyale dan uwansu ya ci gaba da wannan aika-aikar.

A wata takarda ta ranar Juma’a, rundunar ‘yan sanda ta ce ta kama Jude Ogudu, wanda sajan ne da sauran jami’ai guda 4 da aka gani a cikin bidiyon.

Rundunar ta kara da cewa yanzu haka ‘yan sandan 5 suna hannun rundunar ‘yan sandan Edo bangaren binciken masu laifuka (CID) inda ake bincike akan lamarin.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Ogudu ne dan sandan da aka gani a cikin bidiyon ya na cin zarafin matar.

Nasara: Dakarun sojin Najeriya sun sheƙe ƴan ta'adda 49, 863 sun miƙa wuya, DHQ

A wani labari na daban, hedkwatar tsaron kasa ta ce ta halaka 'yan ta'addan 49 a karkashin ayyukan sojojin ta yayin da 'yan ta'addan 863 suka mika makaman su a makonni biyu da suka gabata.

Daraktan yada labarai, Bernard Onyeuko, ya sanar da hakan yayin bayar da bayani kan ayyukan sojojin a ranar Alhamis a Abuja, Premium Times ta ruwaito.

Onyeuko ya ce sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun halaka 'yan ta'adda 37, sun cafke 17 tare da samo miyagun makamai 117.

Asali: Legit.ng

Online view pixel