Da dumi-dumi: Masarautar Bauchi ta tsige Dogara daga sarautarsa saboda dalilai

Da dumi-dumi: Masarautar Bauchi ta tsige Dogara daga sarautarsa saboda dalilai

  • Masarautar Bauchi ya tsige Yakubu Dogara daga sarautarsa ta Jakadan Bauchi bisa zargin kitsa hari kan sarkin Bauchi
  • An ruwaito cewa, an kai wa sarkin Bauchi da na Dass hari, lamarin da ya tunzura masarautar ta Bauchi
  • Masarautar ta zargi Dogara da kitsa harin, wannan yasa aka tsige shi har zuwa lokacin da kotu za ta yi hukunci

Jihar Bauchi - Majalisar masarautar Bauchi ta dakatar da tsohon kakakin majalisar wakilai, Hon. Yakubu Dogara, daga rike sarautar gargajiya na Jakadan Bauchi, Leadership ta ruwaito.

Dakatarwar ta biyo bayan harin da aka kaiwa sarakunan Bauchi da Dass, Alhaji Rilwanu Sulaimanu Adamu da Alhaji Usman Bilyaminu Othman, a ranar 31 ga watan Disamba, 2021 a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Bogoro.

Kara karanta wannan

Watanni bayan dakatar da ita, Hadiza Bala Usman ta ga shugaba Buhari

Yakubu Dogara ya rasa kujerar sarauta
Da dumi-dumi: Masarauta a Bauchi ta tsige Dogara a sarautar da ta bashi | Hoto: dailytrust.com
Asali: Depositphotos

An ce an kai musu harin ne a lokacin da suke kan hanyarsu domin halartar taron tunawa da Baba Gonto karo na 21 da kaddamar da wani littafi.

Da yake zantawa da manema labarai a Bauchi a ranar Litinin din da ta gabata, Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaimanu Adamu, ya ce dakatarwar ta nan take ce har sai an yanke hukunci a gaban kotu, inda Dogara ke fuskantar shari’a da sauran wadanda ake tuhuma.

Sarkin wanda ya samu wakilcin Galadiman Bauchi, Sa’idu Ibrahim Jahun, ya ce abin takaici ne yadda ake zargin Dogara na daya daga cikin wadanda suka kitsa harin da aka kaiwa sarakunan Bauchi da Dass.

Jaridar Guardian ta rahoto shi yana cewa:

“A taron masarauta na baya-bayan nan, mun sake duba lamarin, inda muka nuna rashin jin dadinmu da cewa daya daga cikin ‘ya’yan yankin, mai ruwa da tsaki kuma mai rike da sarautarmu ta gargajiya da aka ambata a matsayin wanda ya yaudari jama’a tare da aikata lamarin.

Kara karanta wannan

Labari ne mai ban tsoro - Dattawan arewa sun yi Allah wadai da kisan Hanifa

“Abin mamaki shi ne bai jajanta ba, ballantana ya nuna nadamar abin da ya faru da masu Martabanmu, sarakunan Bauchi da Dass.
“Saboda haka Majalisar Masarautar ta yanke shawarar dakatar da sarautarsa na Jakadan Bauchi har sai lokacin da kotu ta yanke hukunci.”

Rawanin Sarkin Misau ya na lilo saboda ya shirya taron ‘yan jam’iyyar APC’ a jihar Bauchi

A wani labarin, rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulqadir Mohammed, ya aika wa Mai martaba Sarkin Misau, Ahmed Sulaiman sammaci.

Daily Nigeria ta ce an aikawa Mai martaba Ahmed Sulaiman takardar sammaci saboda zargin shirya taron da ake ganin ya na da burbushin siyasa a Misau.

An gudanar da wannan taro da na-kusa da Mai girma gwamna Bala Mohammed su ke ganin ‘gangamin ‘yan adawa’ a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel