Rawanin Sarkin Misau ya na lilo saboda ya shirya taron ‘Yan jam’iyyar APC’ a jihar Bauchi
- Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed ya aika takardar sammaci ga Sarkin Misau
- Sarkin Misau, Ahmed Sulaiman ya shirya wani taro ba tare da iznin Gwamnati ba
- Wasu manyan jagororin ‘Yan APC ne su ka halarci wannan taro da aka yi a Misau
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulqadir Mohammed, ya aika wa Mai martaba Sarkin Misau, Ahmed Sulaiman sammaci.
Daily Nigeria ta ce an aikawa Mai martaba Ahmed Sulaiman takardar sammaci saboda zargin shirya taron da ake ganin ya na da burbushin siyasa a Misau.
An gudanar da wannan taro da na-kusa da Mai girma gwamna Bala Mohammed su ke ganin ‘gangamin ‘yan adawa’ a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli, 2021.
Sarakunan Keffi da na Nasarawa, Shehu Yamusa da Ibrahim Jibrin sun samu halartar wannan taro.
Daga cikin wadanda su ka je wurin wannan taron akwai tsohon gwamnan jihar Nasarawa, kuma daya daga cikin manyan Sanatocin APC, Abdullahi Adamu.
Taron da aka gudanar a Misau
Kwanaki Sarkin ya rubuta takarda zuwa ga gwamnatin jiha, ya sanar da ita cewa zai shirya taro a kan rawar da masarautar gargajiya ta ke wajen gudanar da mulki.
Gwamnati ba ta ba Sarkin amsar wasikarsa ba, amma duk da haka ya shirya wannan taro da na cikin gwamnati su ke yi wa kallon gangamin ‘yan jam’iyyar APC.
A wajen wannan taro, wasu daga cikin masu magana sun soki gwamnnatin PDP, sannan wadanda suka halarci taron ba su ziyarci Mai girma gwamna ba.
Ba don sa bakin wasu manya ba, jaridar ta ce da a yau gwamnatin jiha za ta tunbuke Sarkin daga kan sarauta. Yanzu haka ana ta kokarin lallabar gwamna Mohammed.
Alakar Sarkin Misau da Gwamnati
Alhaji Ahmed Sulaiman ya dare kujerar sarauta ne bayan mutuwar Sarkin Misau, Alhaji Muhammadu Manga III a Agustan shekarar 2015, a lokacin mulkin APC
Kafin ya zama Sarki, Mai martaban ya rike mukamin shugaban ma’aikatan gwamnatin Bauchi tsakanin 1996 da 1999, bayan nan ne sai yayi ritaya daga aikin gwamnati.
Ahmed Sulaiman ya dawo gwamnati har ya rike kujerar sakataren gwamnatin jiha a mulkin APC. Sulaiman ya na rike da wannan kujera ne aka zabe shi a matsayin sarki.
Ba wannan ne karon farko da Sarkin ya samu matsala ba, a baya Bala Mohammed ya dakatar da shi.
A makon da ya gabata ku ka ji cewa shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya tattara wasu ‘Yan Majalisa sun je Daura wajen yi wa shugaban kasa yawon sallah.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin 'yan majalisar da wasu ‘yan siyasa a gidansa. Daga cikin wadanda suka ziyarce sa har da Gwamna Dave Umahi.
Asali: Legit.ng