Mun tuba, mun dena tada rikici: Tsaffin tsagerun Niger Delta sun roƙi kamfanoni su dawo yankin

Mun tuba, mun dena tada rikici: Tsaffin tsagerun Niger Delta sun roƙi kamfanoni su dawo yankin

  • Tubabin shugaban kungiyoyin tsagerun Neja Delta sun yi kira ga kamfanoni da masu saka hannun jari su dawo yankin
  • Tsafin tsagerun sun ce sun rungumin shirin afuwa ta shugban kasa kuma suna son kamfanonin su dawo domin samun cigaba da ayyuka a yankin
  • Har wa yau, sun kuma nuna rashin jin dadinsu game da yadda ake samun yawaitan haramtattun matatun man fetur da ke hatsari ga al'umma

Bayelsa - Tsaffin tsagerun Neja Delta sun bukaci kamfanonin da yan kasuwa da suka fice daga yankin saboda hare-hare su dawo, suna cewa sun yanke shawarar tabbatar da tsaro mai dorewa a yankin, Daiily Trust ta ruwaito.

Tsaffin shugabannin tsagerun, wadanda suka yi kira ga kamfanoni su yi aiki tare da su domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban yankin, sun yi tir da yawaitan haramtattun matatun man fetur a yankin suna kokawa da illar da suke yi wa lafiyar mutane.

Kara karanta wannan

Samun man fetur ya yi wahala, jama'a sun koka, sun ce za su fara zanga-zanga

Mun tuba, mun dena tada rikici: Tsaffin tsagerun Neja-Delta sun roƙi kamfanoni su dawo yankin
Taswirar yankin Neja Delta. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Da su ke magana a Yenagoa, babban birjin Jihar Bayelsa a karshen mako yayin taron zaman lafiya na yankin, tubabbun tsagerun sun ce zaman lafiya na da muhimmanci wurin ganin masu saka hannun jari sun dawo yankin.

Daya cikin wadanda suka hallarci taron kuma tsohon mai rajin neman yanci, Pastor Nature Dumale Kieghe, ya ce a matsayinsa na tsohon dan gwagwarmaya da ya rungumi shirin afuwa na shugaban kasa, karkashin Col. Milland Dixon Dikio, (mai ritaya), sun yanke shawarar aiki don samar da zaman lafiya a Neja Delta.

Ga wani sashi na jawabinsa:

"Yana da muhimmanci mu wayar da kan mutanen mu game da samar da zaman lafiya a Neja Delta tare da samar da yanayi na zaman lafiya da zai janyo hankalin masu saka hannun jari zuwa yankin.

Kara karanta wannan

Zamfara APC: Rikici ya dauka sabon salo, ana amfani da 'yan daba wurin kai farmaki

"Mu, da a baya muka dauki bindiga, mun zo yanzu muna wa'azin cewa mutanen mu su zauna lafiya.
"Zaman lafiya shine hanyar kadai da za a iya samun cigaba, zaman lafiya ne kadai zai janyo masu saka hannun jari daga da kamfanonin kasashen waje kuma mutanen mu su samu aiki.
"Ya kamata kamfanoni da suka bar bar Neja Delta saboda rashin tsaro su dawo, wannan shine dalilin wannan taron na wayar da kai."

Daily Trust ta rahoto cewa matasa fiye da 150 ne daga yankin na Neja Delta suka hallarci taron wayar da kan da Jihar Bayelsa kuma ana fatan za a yi irinsa a sauran jihohin yankin.

Kungiyar Kirista Ta Najeriya Ta Buƙaci Buhari Ya Janye Tallafin Man Fetur Kafin 2023

A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Kirista ta Najeriya, NCF, gammayar mabiya Katolika da Protestant ta ce ya zama dole gwamnatin tarayyar Najeriya ta jajirce ta ceto kasar daga rushewa ta hanyar cire tallafin man fetur, .

Kara karanta wannan

Nasara: Gwarazan sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutane

NCF ta ce akwai alamu kwarara da ke nuna cewa idan an cire tallafin man fetur, da aka ce yana lashe kimanin Naira biliyan 250 duk wata, tattalin arzikin zai shiga mummunan hali, Guardian ta ruwaito.

A wani taron manema labarai a Abuja, shugaban NCF, Bishop John Matthew, tare da sauran shugabannin kungiyar, sun ce tallafin man fetur babban kallubale ne da ya kamata a tunkare shi gadan-gadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel