Da duminsa: Shugaban PDP, tsaffin gwamnoni, jiga-jigan siyasa sun shiga ganawar sirri da Obasanjo

Da duminsa: Shugaban PDP, tsaffin gwamnoni, jiga-jigan siyasa sun shiga ganawar sirri da Obasanjo

  • Yayinda ake shirye-shiryen zaben shugaban kasan 2023, yan siyasa sun fara bibiyan wadanda suka dade a wasar
  • Shugabannin jam'iyyar adawa ta PDP sun dira gidan tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo
  • Obasanjo na daga cikin wadanda suka assasa jam'iyyar PDP bayan dawowar demokradiyya Najeriya a 1999

Shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Iyorchia Ayu, tsaffin gwamnoni hudu, mambobin kwamitin gudanarwa sun shiga ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Jiga-jigan siyasan sun dira gidan Obasanjo dake Abeokuta, birnin jihar Ogun ranar Asabar misalin karfe 12:25 na rana, rahoton PremiumTimes.

Wadanda ke hallare a ganawar tare da Shugaban PDP sun hada da dan takaran kujeran mataimakin shugaban kasa a 2019, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Sule Lamido, da tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko.

Kara karanta wannan

Ba zan taba komawa jam'iyyarku ba, Obasanjo ya bayyanawa jiga-jigan PDP

Sauran sune, tsohon gwamnan Cross River, Liyel Imoke da tsohon gwamnan Cross River Donald Duke da mataimatin shugaban jam'iyyar PDP (Kudu), Taofeek Arapaja, dss

Da duminsa: Shugaban PDP, tsaffin gwamnoni, jiga-jigan siyasa sun shiga ganawar sirri da Obasanjo
Da duminsa: Shugaban PDP, tsaffin gwamnoni, jiga-jigan siyasa sun shiga ganawar sirri da Obasanjo
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Janar Abdulsalami: Na faɗa wa Obasanjo kada ya shiga siyasa

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) ya bayyana yadda ya shawarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kada ya shiga siyasa bayan jim kadan bayan sako shi daga gidan yari.

Obasanjo, wanda gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta tsare, ya samu yanci ne bayan da Abdulsalami ya hau mulki.

Daga bisani, Abdulsalami ya mika mulki da Obasanjo bayan an zabe shi shugaban kasa a 1999.

Bayan hakan, wasu masu suka sun zargi Abdulsalami da kakabawa 'yan Najeriya, Obasanjo, Janar din soja mai murabus a matsayin shugaban kasa.

Amma a hirar da aka yi da shi a Trust TV, Abdulsalami ya karyata hakan, inda ya bada labarin yadda jim kadin bayan sakinsa ya shawarci Obasanjo kada ya shiga siyasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kwara ta haramta bara a jihar, ta yi yarjejeniyar da al'ummar Hausawar Ilori

Asali: Legit.ng

Online view pixel