Atiku Ya Shiga Rudani Bayan Da Jiga-Jigansa Na Yankin Arewa Maso Gabas Suka Barshi

Atiku Ya Shiga Rudani Bayan Da Jiga-Jigansa Na Yankin Arewa Maso Gabas Suka Barshi

  • Tsohon mataimakin gwamnan jihar Gombe Iliya, kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP ya fice daga jam'iyyar zuwa APC
  • Atiku Abubakar Ya rasa Jamilu Gwamna wanda yake ko'odinetan yakin zabensa a jihar gombe da ke arewa maso gabas
  • Arewa maso gabas dai ita ce cibiya ko kuma yankin da Atiku Abubaka ke takama da shi sabida daga yankin ya fito, kuma akwai gwamnoni uku na jam'iyyarsa.

Gombe: Wasu jiga-jigan siyasar Alhaji Atiku Abubakar guda biyu a yankin Arewa maso Gabas a jiya sun yi watsi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu.

Wa'danda atikun ya rasa sun ha'da da Alhaji Jamilu Gwamna wanda shi ne ko'odinetan na Arewa maso Gabas na kungiyar yakin neman zaben Atiku, da kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Gombe, Charles Iliya.

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Gwamna, Shugaban Matasan PDP Na Shiyya da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

Atiku
Atiku Ya Shiga Rudani Bayan Da Jiga-Jigansa Na Yankin Arewa Maso Gabas Suka Barshi Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauya shekar dai na zuwa ne a ranar da jam’iyyar APC ta fara yakin neman zaben 2023 a wasu sassan kasar nan da suka hada da Maiduguri, jihar Borno da kuma Benin a jihar Edo.

Gwamna, wanda kuma shi ne ya zo na biyu a zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP a jihar a watan Mayu, ya shaida wa manema labarai a Gombe cewa bai ga wata makoma ga jam’iyyar a jihar ba saboda rikicin da ya biyo bayan zaben fidda gwani na gwamna.

Da yake magana a kan wannan batu ga wakilin jaridar The Nation, Gwamna ya ce PDP na cike da rikicin cikin gida, rashin shugabanci, rashin mutunta doka da rashin hadin kai.

An bayyana komawar Iliyan, wanda mataimakin tsohon Gwamna Ibrahim Dankwambo ne a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC da kuma na sake zaben Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.

Kara karanta wannan

Atikun Ba Wata Barazana Da Zaiwa Tinubu A Arewa Maso Gabas - Bayero

Da yake jawabi a wajen kaddamar da yakin neman zaben a jiya, Gwamna Yahaya ya sha alwashin kawar da PDP daga jihar. Ya ce yawan masu sauya shekar da aka samu cikin jam’iyyar shaida ce ta yadda PDP ba ta da gurbi a jihar Gombe.

“Za a binne tarihi da labarin kowace jam’iyya a jihar Gombe,” inji shi.

“Ba za a kara samun jam’iyya ba sai jam’iyya daya, APC. A matsayinmu na jam'iyya mai rinjaye, za mu ceto kuma ba mu da tsoro domin mun san Allah yana tare da mu.
“A shekarar 2019, mun samu 19 daga cikin 24 ‘yan majalisa amma yanzu mun kuduri aniyar kawo duka".

Inuwa Ya cigaba da cewa:

“Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne zai zama shugaban Najeriya a 2023 da yardar Allah kuma Muhammadu Inuwa Yahaya zai zama gwamnan jihar Gombe. Sanata Danjuma Goje shi ne dan takararmu na Gombe ta tsakiya, Sanata Sa’idu Alkali shi ne dan takararmu na Gombe ta Arewa, sannan Sanata Joshua Lidani shi ne dan takararmu na Gombe ta Kudu.”

Kara karanta wannan

Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne

Ba zan bar Shettima -Zulum ba

A jiya ne gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce jam’iyyar APC za ta samu nasara a jihar a zaben shekara mai zuwa da rin jaye mafi tsoka.

Zulum ya karbi ragamar mulkin jihar daga hannun Shettima a karshen wa'adinsa na biyu.

“Bani da wata mafita face in ga jam'iyyar APC ta kawo Barno da Nigeria baki 'daya,” in ji Zulum.

Zulum yayi alkawarin yin aiki tukuru domin samar da kashi 95 cikin 'dari na kuri'ar mutanen ga Jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel