Zan kawar da yan ta'adda gaba daya, Buhari ga mutan Kaduna

Zan kawar da yan ta'adda gaba daya, Buhari ga mutan Kaduna

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja, birnin tarayya bayan ziyarar kwana biyu da ya kai jihar Kaduna
  • Shugaban kasan ya baiwa al'ummar jihar Kaduna cewa jami'an tsaro na iyakan kokarinsu wajen kawar da yan bindiga
  • Jihar Kaduna na cikin jihohin da suka fi fuskantar hare-haren yan bindiga masu garkuwa da mutane

Kaduna - Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatarwa al'ummar jihar Kaduna cewa jami'an Sojin Najeriya zasu murkushe yan bindiga da yan ta'addan da suka addabi jihar da sauran jihohin Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a jawabin da ya saki ranar Juma'a, ya ce Buhari ya bayyana hakan ne a walimar da gwamnatin Kaduna ta shirya masa.

Shugaba Buhari ya jinjinawa Gwamnan jihar Kaduna bisa gudunmuwan da yake baiwa jami'an tsaro musamman kafa ma'aikata ta musamman kan lamarin tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kwara ta haramta bara a jihar, ta yi yarjejeniyar da al'ummar Hausawar Ilori

Yace:

"Ina son tabbatarwa al'umma da gwamnatin jihar Kaduna cewa Gwamnatin tarayya na iyakan kokarinta wajen dakile yan ta'addan da suka addabi jama'a da dukiyoyinsu a sassan kasa."
"A madadin gwamnatin tarayya, ina jinjinawa kokarin gwamnatin jihar Kaduna bisa ayyukan cigaba da tayi."

Zan kawar da yan ta'adda gaba daya, Buhari ga mutan Kaduna
Zan kawar da yan ta'adda gaba daya, Buhari ga mutan Kaduna Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Watanni bayan dakatar da ita, Hadiza Bala Usman ta ga shugaba Buhari

Dakatacciyar Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa (NPA), Hadiza Bala-Usman ta hadu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, 21 ga watan Janairu.

Watanni takwas kenan bayan da Buhari ya amince da dakatar da Hadiza domin bayar da daman yin bincike mai zaman kansa kan wasu zarge-zarge da ake mata.

An zarge ta da laifin karya ka’idojin kudin gwamnati na NPA a karkashin kulawarta. Tun bayan faruwar haka, sai aka nada Mohammed Bello Koko domin ya jagoranci hukumar a madadinta.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ba zan bari wani ya hada 'yan daba su dauki makami ba, inji Buhari

Leadership ta rahoto cewa wata kila Hadiza ta gana da Shugaban kasar a bayan fage amma dai wannan shine karo na farko da ake ganin hotonsu tare a bainar jama’a tun bayan sanar da dakatarwar tata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel