Yaudara: Bayan wata ɗaya da saurayi ya bai wa mahaifiyar ta ƙoda, ta yi wufff ta aure wani

Yaudara: Bayan wata ɗaya da saurayi ya bai wa mahaifiyar ta ƙoda, ta yi wufff ta aure wani

  • Uziel Martinez, malamin makaranta mazaunin Baja California da ke Mexico, ya sanar da yaudarar da tsohuwar budurwar sa ta yi masa
  • Ya sanar da cewa, ya bai wa mahaifiyar budurwar kyautar koda amma bayan wata daga tak ta aure wani saurayin ba shi ba
  • Duk da ya ce ya na jinyar bayar da kodar da ya yi, ya sanar da cewa bai rike ta da komai ba a ran sa amma kuma an yaudare sa

Wani mutum ya bai wa mahaifiyar budurwar sa kyautar koda amma budurwar ta kare da auren wani saurayin bayan wata daya tak.

Uziel Martinez, wani malami daga kasar Mexico, ya wallafa jerin bidiyoyi inda ya bayar da labarin mummunan al'amarin da ya faru da shi, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Yaudara: Bayan wata ɗaya da saurayi ya bai wa mahaifiyar ta ƙoda, ta yi wufff ta aure wani
Yaudara: Bayan wata ɗaya da saurayi ya bai wa mahaifiyar ta ƙoda, ta yi wufff ta aure wani. Hoto daga thesun.com
Asali: UGC

Mazaunin Baja Californian da ke Mexico ya je TikTok inda ya bayar da labarin yadda ya bai wa mahaifiyar tsohuwar budurwar shi koda.

Kara karanta wannan

Rudani: Anata cece-kuce a Twitter yayin da mahaukaci ya yiwa wani kyautar kudi

Budurwar ta bar shi babu dadewa kuma ta yi wuff ta aure wani a cikin wata daya kacal da rabuwar su, indianexpress.com ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon Martinez ya bazu saboda mutane suna ta jajanta masa kan abinda ya faru.

A yayin martani kan sakonni da ya samu na goyon baya, ya tabbatar wa da jama'a cewa ya na lafiya kalau. Ya kara da cewa ya na samun lafiya kan kodar sa da ya bai wa mahaifiyar budurwar.

Ya jaddada cewa, ba ya rike da kowa kuma bai rike tsohuwar budurwar sa a rai ba duk da cutar da shi da ta yi.

Ya sanar da Mexico Daily News cewa: "Ban rike ta da komai ba... Ni ba abokin ta ba ne amma kuma ba mu tsani juna ba. Na yi wannan bidiyon ne domin TikTok, ba na tunanin zai yi tsanani".

Kara karanta wannan

An dakatar da dagaci kan yi wa budurwa auren dole, cin zarafin mahaifin ta da nada mata duka

Bidiyo da hotunan 'yar Najeriya mai shekaru 61 da ta yi aure a karon farko a Jamus

A wani labari na daban, wata ‘yar Najeriya mai shekaru 61, mai suna Lizzy Taiwo, ta fita daga kasuwar ‘yan mata inda ta zama matar aure cikin kwanakin nan ga babban abokinta Colins.

Instablog9ja ta wallafa hotuna da bidiyoyin bikin wadanda aka ga amaryar da bata taba haihuwa ko kuma aure ba a rayuwarta. An yi auren tsakanin Lizzy da Collins ranar Asabar, 15 ga watan Janairu a can cikin kasar Jamus.

‘Yan uwa da abokan arzikin ma’auratan sun je don taya su murna. An ga yadda Lizzy ta sanya wata farar riga irin ta amare ta na kwasar rawa tare da angon ta a gefen ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel