Wata sabuwa: Nnamdi Kanu ya ce shi ba dan IPOB ba ne, bai ma da alaka da ita

Wata sabuwa: Nnamdi Kanu ya ce shi ba dan IPOB ba ne, bai ma da alaka da ita

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, lauyoyi a kotu sunce Nnamdi Kanu ya musanta kasancewarsa mamban IPOB
  • Lauyan gwamnatin Najeriya, Shuaibu Labaran ne ya bayyana hakan bayan dage karar a jiya Laraba 19 ga Janairu
  • Ana tuhumar Nnamdi Kanu da laifuka akalla 15, wadanda tuni ya musanta, lamarin da ya dauki hankalin lauyoyi

FCT, Abuja - Lauyan gwamnatin Najeriya Shuaibu Labaran Magaji ya bayyana cewa Nnamdi Kanu ya musanta cewa shi dan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB ne a kotu ranar Laraba.

Magaji ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar kotun bayan an dage shari’ar Kanu zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu.

Kotu da Nnamdi Kanu: Ya karyata zamansa dan IPOB
Wata sabuwa: Nnamdi Kanu ya ce shi ba dan IPOB ne, bai ma da alaka da ita | Hoto: GettyImages
Asali: UGC

Magaji, wanda ya kawo shaidu biyu a gaban kotu a ranar Laraba, ya bayyana rashin jin dadinsa na yadda ba a iya fara shari’ar nan take ba, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Kotu ta yi hukunci tsakanin Nnamdi da gwamnati, an ci gwamnati tara

A cewarsa, tawagar masu kare Kanu sun dira kotu da bukatar neman beli da kuma wata takardar neman soke tuhumar da ake yi wa Kanu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Magaji ya kara da cewa Kanu ya musanta cewa shi dan IPOB ne.

The Cable ta ruwaito shi yana cewa:

“Daya daga cikin tuhume-tuhumen da ake zargin wanda ake kara, shine batun Nnamdi Kanu dan kungiyar IPOB ne kuma ya musanta cewa shi dan IPOB ne.
"Hakan yana da matukar ban sha'awa kuma muna kira ga 'yan Najeriya da su jira mu su ga yadda za mu tabbatar da duk wadannan tuhume-tuhumen da ake tuhumar wanda ake tuhuma nan da wani lokaci mai zuwa."

Kotu ta yi hukunci tsakanin Nnamdi da gwamnati, an ci gwamnati tara

A wani bangaren, wata babbar kotu a Umuahia ta umurci gwamnatin tarayya da sojojin Najeriya da su biya shugaban 'yan IPOB, Nnamdi Kanu N1bn bisa laifin mamaye gidansa a watan Satumban 2017, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023

Hakazalika, an umarci gwamnatin tarayya da Sojoji da su nemi gafarar Kanu bisa take masa hakkinsa na dan adamtaka.

Mai shari’a Benson Anya ya bayar da wannan umarni ne a yau a lokacin da yake yanke hukunci kan karar da Kanu ya shigar a kan gwamnatin tarayya da sojoji da sauran su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel