Yayinda aka kashe mutum 220 a jihar Neja, Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kai Kasar Dubai

Yayinda aka kashe mutum 220 a jihar Neja, Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kai Kasar Dubai

  • Yan awaren Houthi dake kasar Yaman sun kai mumunan hari kasar UAE inda mutum uku suka rasa rayukansu
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da wannan hari da yan awaren suka kai
  • Wannan ya biyo bayan jawabin Gwamnan Neja inda yace a cikin makonni biyu an kashe mutum 200 a jiharsa

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon jaje ga Gwamnatin haddadiyar daular larabawa UAE bisa harin makami mai linzami da aka kai kusa da birnin Abu Dhabi, babbar birnin kasar.

Tsokaci kan harin da aka kai ranar Litinin, shugaba Buhari ya ce ire-iren wadannan hare-hare ya haddasa hallakan rayuka da asarar dukiyar gwamnati.

Buhari ya jajantawa al'ummar kasar kuma ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su dau mataki.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa.

Kara karanta wannan

Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

Buhari yace:

"A madadin gwamnati da al'ummar Najeriya, muna matukar alhini da jajantawa al'ummar kasar UAE."

Kasar Dubai
Yayinda aka kashe mutum 200 a jihar Neja, Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kai Kasar Dubai Hoto: © Yahya Arhab/EPA/Shutterstock
Asali: UGC

Yan awaren Houthi sun kai hari UAE

A ranar Litinin, yan awaren Houthi sun kai hari da makami mai linzami kasar UAE wanda ya kashe akalla mutum uku, gwamnatin jihar ta bayyana.

Gwamnatin tace hare-hare biyu aka kai kuma ta lashi takobin daukar fansa.

Sani Bello: An fuskanci Farmaki 50, asarar rayuka 220 a Niger cikin watan Janairu

A wani labarin kuwa, Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya bayyana yadda a kalla fararen hula 165, jami’an tsaro 25 da ‘yan Sa Kai 30 suka rasa rayukan su cikin kwanaki 17 na farkon shekarar nan.

Gwamnan ya sanar da wannan yawan ne bayan kammala taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

A cewar sa, ‘yan ta’adda sun kai farmaki 50 a jihar sa wanda ya janyo rashe-rashen rayuka tsakanin ranar 1 ga watan Janairu zuwa 17 yayin da suka afka garuruwa 300 cikin lokacin, inda suka yi garkuwa da mutane 200 ciki har da ‘yan China.

Asali: Legit.ng

Online view pixel