Ayiriri: Gwamnatin Kano ta zuge farashin rijista da sabunta lasisin 'yan adaidaita

Ayiriri: Gwamnatin Kano ta zuge farashin rijista da sabunta lasisin 'yan adaidaita

  • Gwamnatin jihar Kano ta zabge farashin rijistar sabon adaidaita sahu da kuma na sabunta lasisin matukan a jihar
  • Gwamnatin Kano ta mayar da kudin sabuwar rijista zuwa N12,000 daga N18,000, inda na sabunta lasisi ya koma N5,000 a maimakon N8,000
  • An yi wannan yarjejeniyar ne a wani taro tsakanin gwamnatin jihar da lauyoyin masu adaidaitan inda aka kwashe kusan sa'o'i shida

Kano - Matukan adaidaita sahu da gwamnatin jihar Kano a yammacin Laraba sun cimma matsaya a kan yarjejeniyar kudin rijistar sabbin matukan adaidaita sahu da kuma masu sabunta lasisi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, matukan adaidaita sahu a jihar sun yi yajin aikin jan kunne na tsawon kwanaki uku domin nuna fushin su kan sabon harajin da aka kallafa musu.

Kara karanta wannan

Zamfara APC: Rikici ya dauka sabon salo, ana amfani da 'yan daba wurin kai farmaki

Ayiriri: Gwamnatin Kano ta zuge farashin rijista da sabunta lasisin 'yan adaidaita
Ayiriri: Gwamnatin Kano ta zuge farashin rijista da sabunta lasisin 'yan adaidaita. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An cimma matsayar ne bayan shugabannin kungiyar lauyoyi ta Kano sun shiga lamarin inda aka yi taron kusan sa'o'i shida kuma hukumar KAROTA tare da matukan adaidaita sahu da lauyoyin su suka halarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A taron an yanke hukuncin cewa, hukumar ta zabge dubu uku daga kudin sabunta lasisi wanda a baya ya ke dubu takwas, ya koma dubu biyar a halin yanzu.

Sai kudin sabon rijista an zabge dubu shida, wanda a baya ya ke dubu goma sha takwas ya koma dubu goma sha biyu a yanzu.

Daily Trust ta ruwaito yadda matukan adaidaitan sahun suka janye yajin aikin domin bai wa gwamnatin jihar damar sasanci da su.

Lauyan masu adaidaita sahun, Abba Hikima, ya ce sun janye yajin aikin ne bayan yarjejeniyar da suka yi da gwamnatin kan cewa za a rage kudaden.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta titsiye Supo Shasore, tsohon kwamishinan Legas kan damfarar P&ID

Daily Trust ta ruwaito cewa, kasa da watanni 12, wannan ne karo na biyu da matukan adaidaitan suka fada yajin aiki inda suka bar Kanawa suna takawa da kafafun su.

Kano: Matukan adaidaita sahu sun tafka asarar N300m bayan fadawa yajin aiki

A wani labari na daban, yayin da 'yan adaidaita suka fada yajin aiki wadanda aka fi sani da 'yan sahu ko masu Napep a Kano ranar Litinin, hakan ya janyo asarar tarin dukiya ga jihar, matukan haka zalika miliyoyin kudi ga 'yan kasuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na biyu a cikin shekara 1 da matukan adaidaitan suka tsaida amfani da ita wanda ya janyo ci baya ga tattalin arzirki da walwalar mazauna jihar.

An kiyasta cewa, yajin aikin da suka shiga a ranar Litinin ya janyo a kalla asarar naira miliyan 6 wanda jihar ke samun harajin kowacce rana naira 100 ga kowanne mutukin adaidaita a jihar.

Kara karanta wannan

Kotun afil ta zabi ranar zama kan shari'ar dake tsakanin tsagin APC na Shekarau da Ganduje

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel