Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi kasar Gambia halartan biki

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi kasar Gambia halartan biki

  • Shugaban kasan Najeriya ya tafi kasar Gambia da safiyar Laraba daga birnin tarayya Abuja
  • Buhari ya tafi Gambia bisa gayyatar shugaban kasa Adama Barrow bayan lashe zabe karo na biyu
  • Adama Barrow ya lallasa sauran yan takaran zaben shugaban kasan Gambia

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga tashar jirgin saman kasa da kasa ta Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja da safiyar Laraba, 19 ga watan Junairu, 2022.

Shugaba kasan ya nufi birnin Banjul, kasar Gambia don halartan bikin rantsar da shugaban kasa, Adama Barrow, karo na biyu.

Hadimin shugaban kasa na gidajen talabijin da rediyo, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki kuma Legit ta samu.

Yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari yana daga hannu yayinda yake tashi daga filin jirgin Nnamdi Azikwe kuma ya nufi Gambia don halartan bikin rantsar da shugaba Adama Barrow."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya dira birnin Banjul, kasar Gambia don halartan bikin ranstar da Adama Barrow

Buhari zai lula Gambia domin halartan bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace zai je kasar Gambia domin halartan bikin rantsar da shugaban kasarsu, Adama Barrow, wanda zai dare kujerar a karo na biyu a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce an gayyaci shugaban kasar domin ya zama babban bako a bikin wanda zai samu halartan manyan shugabannin Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel