Jirgin Buhari zai lula Gambia domin halartan bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow

Jirgin Buhari zai lula Gambia domin halartan bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Gambia a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu
  • Buhari zai je Gambia ne domin halartar bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow a karo na biyu
  • Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, shugaban hukumar bayanan sirri, Ahmed Rufai za su yi masa rakiya

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai je kasar Gambia domin halartan bikin rantsar da shugaban kasarsu, Adama Barrow, wanda zai dare kujerar a karo na biyu a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce an gayyaci shugaban kasar domin ya zama babban bako a bikin wanda zai samu halartan manyan shugabannin Afrika.

Kara karanta wannan

Hotunan Buhari yayin da ya ziyarci iyalan Marigayi Shonekan don yi masu ta’aziyya

Jirgin Buhari zai lula Gambia domin halartan bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow
Jirgin Buhari zai lula Gambia domin halartan bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow Hoto: BBC
Asali: Twitter

Shugaba Buhari tare da sauran shugabannin kasashen ECOWAS, sun taka muhimmiyar rawar gani wajen dawo da mulkin damokradiyya a kasar Gambia a 2017 bayan tsohon shugaban kasar, Yahaya Jamme, ya ki mika mulki bayan shan kaye a zaben.

Daga cikin wadanda za su yi masa rakiya akwai ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, shugaban hukumar bayanan sirri, Ahmed Rufai da sauran manyan jami'an gwamnati.

Sanarwar ta kuma ce ana sanya ran dawowar shugaban kasar bayan bikin rantsarwar.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban kasa Buhari zai bar Abuja a ranar Laraba, zuwa Banjul, Jumhuriyar Gambia, domin halartan bikin rantsar da Shugaban kasar Gambia, @BarrowPresident; bayan sake zabarsa a karo na biyu.
"Bisa gayyatar mai masaukinsa, Buhari zai zama bako na musamman a bukukuwan wanda sauran shugabanni a Afirka za su halarta a dakin taro na yanci, Bakau.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP

"Shugaba Buhari tare da sauran shugabannin kasashen ECOWAS, sun taka muhimmiyar rawar gani wajen dawo da mulkin damokradiyya a kasar Gambia a 2017 bayan tsohon shugaban kasar, Yahaya Jamme, ya ki mika mulki bayan shan kaye a zaben.
"Shugaban kasar zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama, Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro Babagana Monguno, Shugaban Hukumar Bayanan Sirri Ahmed Rufai da sauran manyan jami'an gwamnati.
"Ana sanya ran dawowar shugaban kasar cikin kasar bayan bukukuwan rantsarwar."

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, saura kiris abinci ya yi araha a Najeriya

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Najeriya da su kara hakuri kan halin da ake ciki a yanzu na tsadar kayan masarufi.

Buhari ya bayyana cewa yawan abincin da ake nomawa a kasar, musamman fadada noman shinkafa da aka yi, zai karyar da farashin kayan abinci, ta yadda kowa zai iya siyansa.

Kara karanta wannan

2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Tsohon mataimakin gwamnan CBN

Shugaban kasar ya yi magana ne a bikin kaddamar da shirin tallafin shinkafa na Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Monoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) a babban dakin baje kolin kasuwancin kasa da kasa na Abuja, rahoton Leadership.

Asali: Legit.ng

Online view pixel