Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai mummunan hari hedkwatar APC, sun halaka jiga-jigan jam'iyya

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai mummunan hari hedkwatar APC, sun halaka jiga-jigan jam'iyya

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kai mummunan hari ofishin jam'iyyar APC ana tsaka da taron sulhu a jihar Enugu
  • Maharan sun bindige jiga-jigan jam'iyyar guda biyu har lahira, sun sace mutum daya, wasu da dama suna matsanancin hali a Asibiti
  • Ɗaya daga cikin mahalarta taron yace maharan sun farmake su ba zato ba tsammani suna cikin gudanar da taro

Enugu - Wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari wurin taron APC a ƙaramar hukumar Enugu ta kudu, jihar Enugu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Yan ta'addan sun yi wa jiga-jigan jam'iyyar ɓarna, inda suka kashe mutum biyu, kuma suka jikkata wasu da dama, suka yi awon gaba da mutum ɗaya.

Rahotanni sun bayyana cewa mambobin APC din suna tsaka da taron sulhu ne a hedkwatar jam'iyyar dake gunduma ta uku, Obeagu Awkunanaw, yankin ƙaramar hukumar Enugu ta Kudu, ba zato yan bindigan suka kunno kai.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun bindige Basarake a jihar Arewa har lahira a cikin gidansa

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai mummunan hari hedkwatar APC, sun halaka jiga-jigan jam'iyya Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Yan bindigan su akalla Bakwai, sun kutsa ofishin taron kai tsaye, suka kashe mutum biyu nan take, suka yi gaba da mutum ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan lamari ya jefa jam'iyyar APC reshen jihar Enugu cikin yanayin jimami da tashin hankali.

Wane taro ƴaƴan APC ke gudanarwa?

Wata majiya daga cikin mahalarta taron, ya bayyana cewa an kira taron ne domin sasanci tsakanin bangarorin jam'iyyar APC a gundumar, a kokarin da ake na haɗa kai baki ɗaya.

Daily Trust ta rahoto Majiyar tace:

"Ana cikin taro waɗan nan yan ta'addan suka kunno kai, suka bindige tsohon shugaban APC na ƙaramar hukumar Enugu South kuma shugaban matasa na tsagi ɗaya, nan take ya mutu."
"Sun kuma kashe wani mutum ɗaya ɗa bansan ainihin sunansa ba. Sun kuma sace shugaban tsagin APC, Honorabul Monday Ogbonna."

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta titsiye Supo Shasore, tsohon kwamishinan Legas kan damfarar P&ID

"Ɗaya daga cikin mahalarta taron na kwance a Asibiti cikin mawuyacin hali, ba mu san ya zata kasance da shi ba."

A wani labarin kuma Babban ɗan kasuwa a Arewa ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na takarar shugaban ƙasa karkashin APC a 2023

Wani ɗan kasuwa daga yankin Arewa, Moses Ayom, ya rubuta wa shugaba Buhari, wasika domin sanar da shi kudirin takara a 2023.

Ayom, ɗan asalin jihar Benuwai, ya shaida wa shugaba Buhari a wasikar cewa yana fatan maye gurbinsa ne domin ɗora wa daga inda zai tsaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel