Sojoji sun bindige mayakan IPOB tare da tarwatsa sansaninsu a daji, sun kwato makamai

Sojoji sun bindige mayakan IPOB tare da tarwatsa sansaninsu a daji, sun kwato makamai

  • aSojoji sun tarwatsa sansanin kungiyar masu neman kafa Biyafara da kuma na Eastern Security Network (ESN) a Jihar Anambra
  • Dakarun sojin sun kuma bindige wasu mayakan kungiyar ta IPOB sannan suka kwato makamai daban-daban
  • Rundunar ce ta sanar da hakan a ranar Talata, 18 ga watan Janairu, an kuma aiwatar da aikin ne a ranar Litinin

Anambra - Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta yi nasarar tarwatsa sansanin haramtacciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biyafara wato IPOB da na Eastern Security Network (ESN) a wani samame na hadin gwiwa da suka kai tare da sauran hukumomin tsaro.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Talata, 18 ga watan Janairu, ta ce sun aiwatar da aikin ne a dajin Lilu da ke karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Nasara: Gwarazan sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutane

Sojoji sun bindige mayakan IPOB tare da tarwatsa sansaninsu a daji, sun kwato makamai
Sojoji sun bindige mayakan IPOB tare da tarwatsa sansaninsu a daji, sun kwato makamai Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Rundunar ta kuma ce, ayyukan wanda aka gudanar a safiyar ranar Litinin, 17 ga watan Janairu, ya yi sanadiyar kashe wasu yan bindiga bayan sun yi musayar wuta a tsakanin su.

An kwato makamai

Bayan tarwatsa sansanin nasu, sojojin sun kuma yi nasarar kwato bindigar harba-ruga 10, wadanda aka kera a gida guda biyu, kananan bindigogi, gatari da tutocin kungiyar IPOB, wayoyin salula da laftop.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daraktan hulda da jama'a na rundunar soji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya kuma ce an kaddamar da harin ne tare da hadin gwiwar rundunar sojojin sama, rundunar 'yan sandan Najeriya da kuma 'yan sadan farin kaya na DSS.

Mai shari'a ta caccaki DSS, ta ce ka da su kara kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya daya

A wani labarin, mai shari'a ta babbar kotun tarayya da ke Abuja, Binta Nyako, ta umurci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta bari Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar yan awaren IPOB da ya sauya kayayyakinsa.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan Sojojin Najeriya sun yi doguwar musayar wuta da yan bindiga a Kaduna

A baya, Nyako ta umurci DSS da ta bari shugaban na IPOB ya dunga yin wanka a duk lokacin da yake son canja tufafinsa, ya ci abinci yadda ya kamata da kuma gudanar da addininsa.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa a zaman kotu na ranar Talata, 18 ga watan Janairu, Mike Ozekhome, lauyan Kanu, ya yi korafin cewa har yanzu wanda yake karewa baya samun kula mai kyau a hannun DSS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel