Kada ku kuskura ku zabi yan shaye-shaye matsayin shugabanni, Uwargidar Masari ta gargadi yan Katsina

Kada ku kuskura ku zabi yan shaye-shaye matsayin shugabanni, Uwargidar Masari ta gargadi yan Katsina

  • Uwargidar Gwamnan jihar Katsina ta yi kira da al'ummar jihar su san wanda zasu zaba sosai kafin su zabeshi
  • Hajiya Hadiza Bello Masari ta bayyana cewa yawancin matsalolin da ake samu da shugabanni bai rasa alaka da kwaya
  • Hukumar NDLEA na cigaba da samun nasarori wajen damke masu safarar muggan kwayoyi a Najeriya

Katsina - Dr. Hadiza Bello Masari, Uwargidar Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ta yi kira ga al'ummar jihar kada su kuskura su zabi yan shaye-shaye matsayin shugabanni.

Dr Hadiza ta bayyana hakan ne ranar Lahadi yayinda ta kaddamar da cibiyar horo da wayar da kan yan kwaya a garin Musawa, jihar Katsina, rahoton ThisDay.

Tace:

"Yana da muhimmanci mu duba wanda ke takarar neman kujerar mulki don sani ko yana shaye-shaye kafin mu zabeshi."

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da 1.5m da za a kai Kebbi da Kano

"Mu tabbatar da cewa mutumin da zamu zaba ba dan kwaya bane ko wanene shi."

Uwargidar Gwamnan tace yadda wasu yan siyasa ke yi a ofis da kuma irin laifukan da suke tafkawa na da alaka da kwaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Uwargidar Masari ta gargadi yan Katsina
Kada ku kuskura ku zabi yan shaye-shaye matsayin shugabanni, Uwargidar Masari ta gargadi yan Katsina Hoto: @mobilepunch
Asali: Twitter

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da 1.5m da za a kai Kebbi da Kano

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta kama kwayoyi akalla miliyan 1.5 na magunguna irin su Tramadol, Exol-5 da Diazepam da aka loda a Onitsha, jihar Anambra.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, a Abuja.

Mista Babafemi ya ce, magungunan da ke kan hanyar zuwa Yauri a jihar Kebbi, hukumar NDLEA ce ta kama su a Edo, a ranar Juma’a 14 ga watan Janairu.

Hakazalika a ranar ne aka gano kwayoyin Diazepam 425,000 a Segemu, Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel