COVID-19 ta azurta Attajiran Najeriya 3, sun samu karin Naira Tiriliyan 3 a cikin shekara 2

COVID-19 ta azurta Attajiran Najeriya 3, sun samu karin Naira Tiriliyan 3 a cikin shekara 2

  • Binciken The Oxfam in Nigeria ya nuna yadda dukiyar masu kudi ta nunku a annobar COVID-19
  • Masu kudin kasar nan sun samu karin akalla Naira Tiriliyan 2.895 a dukiyarsu cikin shekaru biyu
  • A daidai wannan lokaci kuma talakawa sun kara yawa, mafi yawan mutane sun shiga halin ha’ula’i

FCT, Abuja - Kamfanin Oxfam ya bayyana cewa daga watan Maris a 2020, dukiyar wasu manyan masu kudin kasar nan ta karu da kimanin fam Dala biliyan 6.9.

Daily Trust ta ce arzikin wadannan Attajirai uku ya karu ne a daidai lokacin da sauran al’umma suka kara shiga halin ni – ‘ya su a lokacin annobar cutar COVID-19.

Cikakken bayanin nan ya zo ne a wani rahoto mai taken: “Inequality Kills” -The unparallel action needed to combat unprecedented inequality in the wake of COVID-19.

Kara karanta wannan

Shugaban BUA ya samu kusan rabin Tiriliyan a kwana 7 a lokacin da Dangote ya yi asara

Wannan rahoto mai shafi 59 da aka fitar a ranar Litinin, 17 ga watan Junairu, 2022 a garin Abuja ya nuna irin shan bam-ban da ake samu tsakanin talaka da mai hali.

Shugaban kungiyar nan ta CISLAC watau Auwal Musa Rafsanjani da takwarorinsa na Oxfam in Nigeria; Henry Ushie da Chinedu Bassey suka kaddamar da rahoton.

Talaka
Talaka a titin Kano Hoto: www.cfr.org
Asali: UGC

Mutum 2 sun dama miliyan 60

Kamar yadda jaridar ta fitar da labarin, Dr. Vincent Ahonsi ya ce abin takaici ne yadda arzikin manyan Attajirai biyu a Najeriya, ya zarce na talakawa miliyan 63.

Darektar kungiyar Gabriela Bucher ta ce dukiyar mashahuran Attajiran Najeriya ta karu da 38%, yayin da mutum miliyan 7.4 suka zama talaka tubus a shekarar 2020.

Mutane 4,690 ne suke da akalla Dala miliyan biyar a Najeriya. Sannan kuma akwai masu kudi 245 da abin da suka mallaka ya haura $50m, gaba daya dai sun tara $56.5bn.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da 1.5m da za a kai Kebbi da Kano

Masu kudi sun kara kudi, talaka sun kara tsiyacewa

Wannan rahoto na Oxfam in Nigeria ya nuna arzikin manyan masu kudin Duniya ya nunku fiye da sau biyu a wadannan shekaru da ake fama da annobar Coronavirus.

Daga $700bn, Attajirai goman farko da ake ji da su a fadin Duniya sun ba $1.5trn baya a yau. Hakan ya nuna nufin sun samu $1.3bn a duk rana daga 2020 har zuwa yanzu.

Su kuma talakawa sun kara shiga cikin tasko ne a halin yanzu. Mutane miliyan 160 suka zama talaka a wannan marra bayan sun rasa 99% na duk abin da suka mallaka.

TSA bai hana komai ba

Ku na da labari cewa tun a shekarar 206 ne Gwamnatin Muhammau Buhari ta dabbaka tsarin TSA da nufin rage sata a gwamnati da tabbatar da gaskiya a wajen aiki.

Shekaru shida da kawo wannan tsari, bincike ya nuna har yanzu ma’aikatan su na yin satarsu.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun bindige mayakan Boko Haram sama da 40 a jihar Borno

Asali: Legit.ng

Online view pixel