Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun kai wani mummunan hari Jihar Kebbi, sun ƙona dandazon mutane

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun kai wani mummunan hari Jihar Kebbi, sun ƙona dandazon mutane

  • Yan bindiga sun kai wani mummunan hari ƙauyen Ɗan Kade dake jihar Kebbi, inda suka kashe adadi mai yawa na mutane
  • Wani ɗan ƙauyen, Bello, yace maharan sun kona gawarwakin da yawan mutanen da suka kashe, kuma sun ƙona gidaje
  • Hukumar yan sanda tace jami'inta ɗaya da kuma sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin harin

Kebbi - Mutane da dama sun mutu yayin wani mummunan hari da yan bindiga suka kai ƙauyen Ɗan Kade, dake yankin Unashi, ƙaramar hukumar Zuru a jihar Kebbi, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Wasu tsagerun yan ta'adda masu ɗimbin yawa ne suka mamaye kauyen da tsakiyar daren ranar Lahadi, inda suka hallaka dandazon mutane.

The Cable ta ruwaito cewa jami'in hukumar ɗan sanda guda ɗaya, da sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin harin.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Rikicin APC ya kara kamari, daraktan kungiyar gwamnoni ya yi murabus

Jihar Kebbi
Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun kai wani mummunan hari Jihar Kebbi, sun ƙona dandazon mutane Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin ƙauyen, Bello Dankade, ya bayyana cewa yan ta'addan sun kashe mutane da yawa, kuma suka ƙona gawarwakin su.

Punch ta rahoto Bello yace:

"Sun kashe mutane da yawa kuma suka ƙona gawarwakin su. A halin yanzu ba zamu iya tabbatar da yawan mutanen da aka kashe ba."
"Muna mamakin yadda ayyukan ta'addanci ke cigaba da ƙaruwa, musamman a yankin arewa maso yammacin Najeriya."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Litinin.

Kakakin yan sandan yace:

"Wasu yan bindiga sun farmaki ƙauyen Ɗan Kade, kuma dama can mun tura jami'an tsaron mu yankin. Da samun rahoton harin jami'an suka kira waya, aka haɗa sojoji da yan sanda suka kai ɗauki."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga: Abinda Gwamna Masari ya faɗa wa Bola Tinubu kan kawo karshen rikici a jihar Katsina

"Abin baƙin cikin shi ne, yayin musayar wuta ɗan sanda ɗaya da sojoji biyu sun rasa rayukan su. Sannan kuma maharan sun kashe fararen huta mutum 13."
"Bayan haka yan bindigan sun sace mutane da dama, kuma sun kona gidajen mutane a ƙauyen."

A wani labarin kuma Mun kawo muku bayanan da ya kamata ku sani game da filin yakin Mbormi, wurin da tsohon sarkin Musulmai Attahiru ya yi shahada a kokarin kare Masarautar Sheikh Bin Fodio

Sheikh Usman Ɗan Fodio, babban malami ne da musulmai ba zasu mance da jihadinsa ba a Najeriya har ya kafa masarautar Musulmai a Sokoto.

Sai dai Khalifa na 12 bayan rasuwar Ɗan Fodio, Sultan Attahiru. ya rasa rayuwarsa ne a kokarin kare martabar Masarautar kakansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel