Nasarawa: Yadda mata ta daba wa miji wuka har lahira saboda amsa wayar budurwa
– Wata matar aure a jihar Nasarawa ta kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka saboda ya amsa wayar budurwa
– Veronica, mai shekaru 22 da haihuwa ta ce nufinta shine razana marigayin mijin ta ya mika mata wayarsa amma tsautsayi ta shiga
– Matar wacce tace tana dauke da juna biyu na wata daya ta yi nadamar abinda ta aikata tare da cewa sharrin shedan ne kuma ta nemi rangwame
Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Nasarawa ta kama wata mata mai juna biyu mai shekaru 22, Veronica Boniface, saboda kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka saboda ya amsa wayar budurwarsa.
Da ake holen wacce ake zargin a hedkwatan hukumar a Lafia, Kwamandan NSCDC a jihar, Habu Fari, ya ce an kama matar ne a garin Obene a karamar hukumar Keana bayan samun bayanan sirri.
KU KARANTA: Borno: Sabon Shehun Bama ya kai wa Gwamna Zulum ziyarar ban girma (Hoto)
Fari ya yi bayyanin cewa gwaje gwajen da likitoci suka yi wa wanda ake zargin ya nuna cewa ba ta da tabin hankali kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Kwamandan ya kara da cewa idan hukumar ta kammala bincike za ta gurfanar da wacce ake zargin a gaban kuliya.
"An garzaya da mijinta zuwa asibiti bayan ta daba masa wuka sakamakon cacan bakin da suka yi saboda tana zargin wata budurwa ta kira shi a waya.
"Mun gano cewa tana da mai shekaru biyu da rabi da yanzu ya ke hannun dangin marigayin mijinta, Mohammed," kamar yadda Mr Fari ya bayyana.
Da ta ke zantawa da manema labarai, Veronica ta ce ta yi nadamar abinda ta aikata kuma ta roki ayi mata rangwame.
Wacce ake zargin ta bayyana cewa tana dauke da juna biyu na wata daya da ta samu tare da marigayin mijin ta.
Ta kara da cewa sharrin shedan ne yasa ta aikata kisar, inda ta ce niyyar ta shine ta razana mijin ya mika mata wayar salular amma kuma lamarin ya juye ya yi sanadin mutuwarsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng