Sana’ar duka tsofaffin shugabannin kasa 13 da aka yi a tarihi daga shekarar 1957 zuwa 2019

Sana’ar duka tsofaffin shugabannin kasa 13 da aka yi a tarihi daga shekarar 1957 zuwa 2019

  • An yi shugabannin kasa fiye da 10 daga lokacin da aka yi zaben farko a Najeriya zuwa shekarar 2019
  • Abubakar Tafawa-Balewa ne shugaban farko wanda ya rike Firayim Minista, asalinsa malamin makaranta ne
  • Yakubu Gowon da Obasanjo sojoji ne da suka yi mulki, bayan sun sauka sun je jami’a sun kara karatu

A wannan rahoto, mun tattaro sana'ar da tsofaffin shugabannin suka yi gabanin hawansu mulki"

1. Abubakar Tafawa Balewa – Malamin makaranta

Sir Abubakar Tafawa-Balewa shi ne Firayim Minista na farko kuma na karshe da aka yi a tarihin Najeriya. Kafin ya zama shugaba a 1957, ya yi aiki ne a matsayin malamin makaranta.

2. Jonathan Aguiyi-Ironsi – Soja

Bayan kashe Tafawa-Balewa a 1966 wanda ya gaje shi, shi ne Janar Jonathan Aguiyi-Ironsi. Ironsi yana cikin wadanda suka fara shiga soja a tarihin Najeriya, kuma na farko da ya yi mulki.

Kara karanta wannan

Addini, rashin lafiya, da matsaloli 5 da Tinubu zai fuskanta a neman Shugaban Najeriya

3. Yakubu Gowon - Soja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A watan Yulin 1966 aka samu soja ya gaji mulki a hannun takwaransa soja. Gowon bai da wani sana’a face aikin soja. Bayan an hambarar da shi a 1976, ya je jami’a ya yi Digirin PhD.

4. Murtala Mohammed – Soja

Kamar sauran iyayen gidansa da suka yi shekaru sama da 10 a kan mulki, Janar Murtala Ramat Mohammed soja ne wanda ba a san shi da wani aiki ba sai kare martabar Najeriya.

5. Olusegun Obasanjo – Soja/Manomi

Olusegun Obasanjo ya hau kan mulki bayan mutuwar Murtala. Shi ma dai Injiniyan soja ne, daga baya ya rungumi harkar noma. Bayan ya sauka a mulki, shi ma ya koma makaranta.

6. Shehu Shagari – Malamin makaranta/jami’i/manomi

Alhaji Shehu Usman Shagari wanda ya lashe zaben 1979, ya zama shugaban Najeriya malamin makaranta ne, kuma ya rike mukamai da-dama a gwamnati baya ga zamansa manomi.

Kara karanta wannan

Atiku, Kwankwaso, da mutane 10 da za su iya bayyana niyyar tsayawa takara bayan Tinubu

7. Muhammadu Buhari – Soja/Makiyayi

Janar Muhammadu Buhari shi ne soja na biyar da ya yi mulki a Najeriya. Duk da soja ne shi, an san shugaba Buhari da kiwon dabbobi a gidansa da ke garin Daura, jihar Katsina.

Tsofaffin shugabanni
Tsofaffin shugaban kasa
Asali: UGC

8. Ibrahim Badamasi Babangida - Soja

Janar Ibrahim Badamasi Babangida wanda ya yi nasarar kifar da Buhari a mulki soja ne kamar mai gidansa. Ba a san shi da wani aiki kafin 1985 ba, daga baya ya zama 'dan siyasa.

9. Ernest Shonekan - 'Dan kasuwa

Ernest A.O Shonekan ne ya zama shugaban rikon kwarya a 1992. Ko da Cif Shonekan Lauya ne, ya zama ‘dan kasuwa wanda ya yi suna a kamfanin United African Company of Nigeria.

10. Sani Abacha - Soja

Janar Sani Abacha wanda ya yi juyin-mulki na karshe a Najeriya, sojan yaki ne. Mahaifinsa da iyalinsa sun yi kasuwanci, amma ba a san shugaban da wani sana’a ba sai soja.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Diyar sarki ta rasu kwanaki kadan bayan rasuwar mahaifinta

11. Abdussalami Abubakar - Soja

Bayan mutuwar Sani Abacha, wani sojan ne dai ya karbi mulki na gajeren lokaci. Janar Abdussalami Abubakar soja ne kamar sauran iyayen gidansa da suka yi mulkin kasar.

12. Olusegun Obasanjo

An yi bayani a baya.

13. Ummaru Musa ‘Yar’adua - Malamin makaranta

Ko da kafin ya shiga siyasa, ya yi kasuwanci, Ummaru ‘Yar’adua ne shugaban farko da aka zaba mai shaidar digiri. Kafin zamansa gwamna a 1999, malamin ilmin sinadarai ne a Katsina.

14. Goodluck Jonathan - Malamin jami'a

Dr. Goodluck Jonathan wanda ya gaji ‘Yar’adua bayan rasuwarsa, shi ma malamin jami’a ne a Fatakwal. Jonathan shi kadai ne shugaban Najeriya da ya yi karatu har ya samu PhD.

15. Muhammadu Buhari

An yi bayani a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel