Ministan Buhari ya ce akwai alheri da yawa a yarjejeniyar Twitter da Najeriya

Ministan Buhari ya ce akwai alheri da yawa a yarjejeniyar Twitter da Najeriya

  • Karamin ministan kwadago ya magantu kan matakin gwamnati na dage dokar dakatarwar da ta sanya wa Twitter
  • Festus Kayemo ya bayyana cewa, Najeriya ta samu karuwa da wannan dakatarwar ta hanyoyi da dama
  • Hakazalika, ya caccaki wadanda suka yi ta amfani da Twitter duk da hanin da aka yi, suka fifita siyasa kan kishin kasa

Abuja - Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, SAN, ya ce Najeriya za ta fi morewa da duk wasu sharuddan da ta gindayawa dandalin sada zumunta na Twitter a yanzu.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis bayan gwamnatin shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ta janye dakatarwar shafin Twitter bayan sama da watanni bakwai.

Kara karanta wannan

Dama bamu hanu ba: Martanin 'yan Najeriya bayan dage dokar Twitter

Ministan Buhari ya bayyana alherin rufe Twitter
Ministan Buhari ya ce akwai alheri ya yawa a yarjejeniyar Twitter da Najeriya | Hoto: punchnh.com
Asali: UGC

A cewar Kayemi:

“Ga wadanda suka fifita siyasa a kan kishin kasa kuma suka nuna rashin gaskiya a kan dakatarwar Twitter, yanzu za su iya ganin cewa tare da duk sharuddan FG da Twitter ya amince da su, Najeriya ta fi samun alheri. Na taya Najeriya murna."

Dalilin dakatar da Twitter

A baya idan baku manta ba, kamfanin Twitter ya goge rubutu kan tuno yadda yakin basasan Najeriya ya kasance a Najeriya da Buhari yayi a watan Yunin 2021, kamar yadda Punch ta rahoto.

Wannan ne dalilin da yasa gwamnati ta dauki matakin dakatar da kafar, tare da bayyana wasu sharruda da tace dole Twitter ya cika su kafin ya ci gaba da aiki a Najeriya.

Rahotanni da dama sun bayyana yadda gwamnatin Najeriya ta tafka asarar makudan kudade ta dalilin dakatar da kafar, amma duk da haka gwamnatin ta dage sai da kamfanin Twitter ya cika ka'ida.

Kara karanta wannan

FG ta bayyana sharudda 5 da ta gindaya wa Twitter kafin dage dokar haramci

A wani labarin, a jiya Laraba ne gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin kamfanonin sadarwa su bude kowa ya ci gaba da amfani da shafin Twitter a Najeriya bayan kwanaki 222 da dakatar dashi.

Dakatarwar dai ta biyo bayan dambarwar da aka samu tsakanin gwamnatin Najeriya da Twitter kan wani rubutu na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A baya gwamnatin Najeriya ta ba da wasu ka'idoji da tace dole Twitter ta cika su kafin daga bisani a bata damar ci gaba da gudunar da ayyukanta a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel