Yajin aikin 'yan adaidaita: PDPn Kano ta zargi Ganduje da shirin karya tattalin arzikin jihar

Yajin aikin 'yan adaidaita: PDPn Kano ta zargi Ganduje da shirin karya tattalin arzikin jihar

  • Jam'iyyar PDP reshen Kano ta yi martani a kan yajin aikin yan adaidaita sahu a jihar
  • PDP ta zargi gwamnan na Kano, Abdullahi Umar Ganduje da shirin karya tattalin arzikin jihar
  • Jam'iyyar adawar ta kuma ce gwamnatin Ganduje bata yiwa bangaren sufuri komai ba tsawon shekaru bakwai da tayi a mulki

Kano - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Kano ta zargi gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da yiwa tattalin arziki zagon kasa kan yajin aikin da yan adaidaita sahu suka tafi.

Ta ce matakin da gwamnatin ta dauka don ta lalata ayyukan tattalin arziki na yau da kullun ne tunda har ta ki sasantawa da yan adaidaitan da ke yajin aiki tsawon kwanaki uku, rahoton Daily Trust.

Yajin aikin 'yan adaidaita: PDPn Kano ta zargi Ganduje ta shirin karya tattalin arzikin Kano
Yajin aikin 'yan adaidaita: PDPn Kano ta zargi Ganduje ta shirin karya tattalin arzikin Kano Hoto: BBC.com
Asali: Twitter

A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar a jihar, Shehu Wada Sagag, jam'iyyar ta ce an san Kano da harkokin kasuwanci daban-daban kuma sufuri shine babban ginshiki inda masu adaidaita ke jigilar akalla kaso 80 na shige da fice a birnin, rahoton Solacebase.

Jawabin ya kara dacewar babban abu ne sanin cewa gwamnatin Ganduje ta gazawa al’ummanta ta koina, musamman gwamnatin jihar bata yiwa bangaren sufuri komai ba tsawon shekaru bakwai da tayi a mulki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ci gaba da cewa a maimakon haka, ta datse tsarin sufurin dalibai na Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

“Ganduje da tawagarsa sun mayar da hukumar KAROTA wata babbar hukumar tattara kudaden shiga maimakon ta zama hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa kamar yadda aka kafa ta.

“Dubban daruruwan matasa ne ke wannan sana’a kuma tana samar da ayyukan yi da kuma kudaden shiga na jiha, gwamnati mara alkibkalar tattalin arziki ce kawai za ta iya yakar matasa, mata da sauran mutane masu dogaro da kai a daidai lokacin da kasar ke fuskantar koma baya ta fuskacin tattalin arziki da rashin tsaro da ya jefa ‘yan kasar cikin matsanancin talauci.”

Jam’iyyar ta kuma ce ya kamata gwamnatin ta gaggauta magance lamarin saboda barin Wannan na iya zama hargitsi da tarwatsa zaman lafiya a jihar saboda lamarin ya bar matasa da yawa babu aikin yi.

Da karhse: Gwamnatin Kano ta samar da hanyar sufuri da za ta maye a daidaita sahu

A gefe guda, mun ji a baya cewa, gwamnatin jihar Kano za ta sharewa mazauna jihar hawaye ta hanyar kaddamar da sabon tsarin sufuri biyo bayan yajin aikin 'yan a daidaita sahu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Manajan daraktan hukumar KAROTA, Baffa Babba-Dan’agundi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan yajin aikin da masu tuka a daidaita sahu a jihar suka yi.

Hakazalika, Baffa ya yi sharhi kan yadda gwamnatin a baya ta sanya kudin rajistar aiki ga 'yan a daidaita a kan kudi N100,000 amma daga baya ta sassauta zuwa kasa da haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel