Bayan amsan N10m hannun saurayi, Bazawara tace ta fasa aurensa ana saura kwana 10 aure

Bayan amsan N10m hannun saurayi, Bazawara tace ta fasa aurensa ana saura kwana 10 aure

  • Rikici ya barke yayinda bazawara tace zata koma gidan tsohon mijinta ana saura kwana 10 aurenta da wani saurayi
  • Daga bisani Saurayin ya maka ta a kotun majistare inda yace ta karbi kudi akalla milyan goma hannunsa
  • Alkalin kotu ya bada belinta tare da wasu sharruda masu tsauri

Wata bazawara mai 'yaya biyu, Fatima Sanusi, ta gurfana gaban kotu kan zargin ta damfari saurayin da aka sanya musu rana N10m kuma tace ta fasa ana sauran kwana 10 aure.

An gurfanar da Fatima Sanusi ne a kotun Majistare dake unguwar Barnawa a jihar Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito cewa an shirya komai don auren amma Fatima tace ta fasa auren Umar Oruma ana saura kwanaki goma a shafa Fatiha, yanzu tana son komawa wajen tsohon mijinta.

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

A Takardar da aka shigar kotu, an ce:

"Mai kara da wacce aka shigar kara sun fara soyayya tun Yulin 2020, kuma bayan tsawon lokaci, ya nemi aurenta a Junairun 2021 kuma ta yarda."
"Sakamakon haka ne ta fara karban kudi hannunsa domin tayi amfani da su wajen kula da kanta, 'yayanta da iyayenta."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bazawara tace ta fasa aurensa ana saura kwana 10 aure
Bayan amsan N10m hannun saurayi, Bazawara tace ta fasa aurensa ana saura kwana 10 aure
Asali: Twitter

Ya kashe sama da milyan 3 wajen shirye-shiryen auren

Takardar tuhumar ta kara da cewa Saurayin ya bata kimanin milyan bakwai kuma ya kashe sama da milyan uku daban wajen shirin aure.

Takardar tace:

"Daga ranar da kika yi alkawarin aurensa, ya kashe N6.7million a kanki kuma ya kashe karin akalla N3.2million don shirye-shiryen aure."

Daga karshe kotu ta bada belinta kan N500,000 da kuma masu tsaya mata mutum biyu.

Daga cikin sharrudan shine mutum daya ya kasance dan'uwanta kuma mai aiki a wata sananniyar ma'aikata, sannan mutum na biyu ya kasance makwabci.

Kara karanta wannan

Tiwa Savage: Na so ace Dangote mahaifi na ne, amma kash

N200 kudin cefane a zamanin nan: Mata ta kai miji kotu kan gallaza mata da yunwa

A wani labarin kuwa Wata matar aure, Basirat Ajayi, ta bayyana wa wata kotun da ke Mapo a Ibadan yadda mijinta, Ajayi Babatunde ke ba ta ita da ‘ya’yansu uku Naira 200 zuwa 500 a matsayin kudin cefane a kullum.

Basirat, wacce ‘yar kasuwa ce, ta ce mijin nata dan buguwa ne da ke shan taba kuma ya kwankwadi barasa kafin ya dawo gida da dare

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel