N200 kudin cefane a zamanin nan: Mata ta kai miji kotu kan gallaza mata da yunwa

N200 kudin cefane a zamanin nan: Mata ta kai miji kotu kan gallaza mata da yunwa

  • Wata mata ta maka mijinta a kotu saboda azabtar da ita da 'ya'yanta da yunwa, kamar yadda ta shaidawa kotu
  • Ta ce, mijin nata bai damu da daukar nauyinta da na 'ya'yanta uku ba, don haka take son a raba aurensu
  • Mijin shi kuwa, ya bayyana wasu halayen matar da yace shi sam ya gaji da halayenta, don haka shi ma ya nemi a raba auren

Ibadan, Oyo - Wata matar aure, Basirat Ajayi, ta bayyana wa wata kotun da ke Mapo a Ibadan yadda mijinta, Ajayi Babatunde ke ba ta ita da ‘ya’yansu uku Naira 200 zuwa 500 a matsayin kudin cefane a kullum.

Basirat, wacce ‘yar kasuwa ce, ta ce mijin nata dan buguwa ne da ke shan taba kuma ya kwankwadi barasa kafin ya dawo gida da dare, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma

Rikicin aure a jihar Oyo saboda cefane
N200 kudin cefane a zamanin nan: Mata ta kai miji kotu kan gallaza mata da yunwa | Hoto: channelstv.com
Asali: Twitter

Ta ce surukarta ta kan yi mata fada, ta kara da cewa duk dangin mijinta suna da mugun hali.

Basirat ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gaskiya aurena da Babatunde hadi ne tsakanin iyayena da nashi.
“Don haka, ba su biya ni kudin aure na ba.
“Bugu da kari, ba ya girmama dangina kuma ba ya daukar nauyin yara.
“Babatunde yakan baiwa yaranmu uku Naira 500 ko N200 ne kacal a matsayin kudin da zai ciyar damu.
“Karshe ma, tun lokacin da na dauke su ya daina ba su.

Da take bayyana dalilin dauke yaran, Basirat ta ce:

"Babatunde ba zai kula da yaran yadda ya kamata ba saboda yana kai su ga mahaifiyarsa da ba ta kula da su."

Ajayi Babatunde, wani ma’aikacin wutar lantarki ne wanda tun da farko ya nemi rabuwa da matarsa saboda yawan mita da korafi, ya ce ba zai iya jurewa kiyayyar da matarsa ​​ke yi masa da danginsa ba.

Kara karanta wannan

Ko shaiɗan ba zai faɗi abubuwan da ake yaɗawa ba, Mummy GO ta ce lalata bidiyoyin ta aka yi

A cewarsa:

“Ranka shi dade, Basirat ta aure ni ne saboda aurena da ita hadi ne tsakanin iyayena da iyayen Basirat.
“Ban shiga cikin dukkan lamarin auren da ya kai ta gidana ba.

“Ban san dalilin da ya sa ta tsani dangina ba saboda ba ta son ganinsu kuma na gaji da kasancewarmu tare.

"Ina son kotu ta ba ni damar kula da yaranmu uku."

Bayan jin batutuwansu, kotunta shawarci ma’auratan da su ci gaba da zaman lafiya zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukunci kan lamarin.

Ta dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga Maris domin yanke hukunci.

Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Wata mata 'yar Nigeria da bata dade da aure ba ta roki kotun Shari'a da ke Samaru, Gusau, jihar Zamfara ta raba aurensu bayan sati ɗaya saboda girman mazakutar mijin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan sanda sun shiga tsakani yayin da kwarto ya kashe mijin daduronsa

The Nation ta ruwaito cewa A'isha Dannupuwa, mai 'ya'ya uku ta shaidawa kotu cewa ta auri mijinta na biyu ne bayan auren ta na farko ya mutu.

A jawabinta, ta ce al'adarsu ne dama ta fara tarewa a gidan iyayensa kafin daga baya ta tare a gidan mijinta, bayan ɗaurin aure.

Ta shaidawa kotu cewa:

"Da ya zo, ya kusance ni amma a maimakon samun natsuwa sai akasin haka ta faru saboda tsabar girman mazakutarsa."

A wani labarin, wani ango ya bayyana aniyarsa na kawo karshen auren da ke tsakaninsa da matarsa kan zargin da ya shiga tsakani.

Labarin da aka yada ya nuna cewa mutumin ya kama matarsa tana sheke ayarta da wani kato kwanaki kadan bayan aurensu.

A cewar labarin da @chuddyOzil ya wallafa a shafinsa na Twitter, mutumin da matarsa sun yi aure ne a ranar 27 ga watan Disamba, 2021. Sai dai rikicin ya soma ne lokacin da mutumin ya kama matarsa da wani mutum a wurin da suke shakatawa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel