Allah ya yiwa Sheikh Yahaya Usman Gidadawa rasuwa a safiyar talata

Allah ya yiwa Sheikh Yahaya Usman Gidadawa rasuwa a safiyar talata

Allah ya yiwa Sheikh Yahaya Usman Gidadawa rasuwa a safiyar talatar nan, Farfesa Mansur Sokoto ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.

Marigayin ya kasance mai jawa Farfesa Mansur Sokoto bakin littafin Sahihul Bukhari.

Ya kara da cewa za'a yi masa Sallar Jana'iza karfe 12 na rana a yau Talata, 11 ga Junairu, 2022 a cikin garin sokoto.

Kungiyar Izala a sakon ta'aziyyarta ta bayyana cewa Marigayin ya rasu bayan fama da jinya.

Ya rasu ya bar mata 4 da yara 40.

Allah ya yiwa Sheikh Yahaya Usman Gidadawa rasuwa a safiyar talata
Allah ya yiwa Sheikh Yahaya Usman Gidadawa rasuwa a safiyar talata Hoto: Mansur Sokoto
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jagora ne a kungiyar Izala

Kafin rasuwar shehin Malamin babban Malami ne a matakin kasa, kuma shine shugaban JIBWIS Social Media ta jihar sokoto, sannan sakataren kungiyar JIBWIS a matakin jiha.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Diyar sarki ta rasu kwanaki kadan bayan rasuwar mahaifinta

Kungiyar JIBWIS tace:

"A madadin Kungiyar IZALA muna mika ta’aziyya ga ‘Yan uwa da iyalai, al’ummar jihar sokoto da kasa baki daya akan wannan rashi, tare da fatan Allah ya jikansa ya gafarta masa, ya kuma shiga cikin lamarin iyalansa, Allah ya hada mu da shi a aljanna firdausi baki Dayan mu."

Addu'o'in Jama'a wa Malamin

Adamu Dahiru Gambo yace:

"Allah ya jikansa, mutanen kirki sunata tafiya azzalumai kuma suna jimawa karshen zamani tazo kusa Allah yasa mu gama da duniya lafiya Ameen"

Haroon Ababakar:

"Allah ya gafarta masa, ya masa rahama, ya Kuma ji kansa"

Shari'u Muhammad:

"Allah ya jikansa da rahma"

Asali: Legit.ng

Online view pixel