2023: Ku samu katikan zaben domin zaben shugabanni nagari, Sanusi

2023: Ku samu katikan zaben domin zaben shugabanni nagari, Sanusi

  • Muhammad Sunusi II, shugaban kungiyar Tijjaniyya ta kasa, ya shawarci ko wanne dan Najeriya da ya tanadi katin zabensa kafin zaben 2023
  • Sunusi ya bayar da wannan shawarar ne a wani taron zagayowar ranar maulidi ta duniya na 4 da su ka yi ranar Asabar a Lokoja, jihar Kogi
  • Tsohon sarkin Kanon ya bukaci ‘yan kungiyar Tijjaniyya da su zage damtsensu wurin ganin sun yi zabe, don haka duk wanda ba shi da katin zabe ya nema

Lokoja, Kogi - Muhammad Sunusi II, shugaban kungiyar Tijjaniyya ta kasa, ya shawarci duk wani dan kasar da shekarunsa su ka kai, ya tanadi katin zabensa kafin shekarar 2023.

Sunusi ya yi wannan furucin ne a ranar Asabar yayin taron zagayowar bikin maulidi na duniya da su ka yi a Lokoja, jihar Kogi, TheCable.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya bayyana wanda APC za ta tsayar idan tana son lashe zabe a 2023

2023: Ku samu katikan zaben domin zaben shugabanni nagari, Sanusi
2023: Ku samu katikan zaben domin zaben shugabanni nagari, Sanusi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Tsohon sarkin Kano ya ce duk wani dan Tijjaniyya ya zage damtse a harkar siyasa, inda yace ko wanne dan Najeriya ya dage ya yi zabe.

Sunusi ya kara da cewa ‘yan kungiyar su dage wurin zaben shugabanni na kwarai kada su duba jam’iyya ko kuma addini, TheCable ta ruwaito.

“Idan matasanmu su ka samu ayyukan yi, gaba daya tattalin arzikin kasar nan zai gyaru,” a cewarsa.
“Kowanne dan kungiyar Tijjaniyya da ya wuce shekaru 18, namiji ko mace ya tanadi katin zabe.
“Ubangiji ya baku umarnin mika amanarku ga mutanen kirki masu amana.
“Yanzu muna lokacin da mutane su ke da damar daura mutum a kan karagar mulki, zabenka ‘yancin ka.
“Ban ce ‘yan kungiyar Tijjaniyya kadai za ku zaba kadai ba ko kuma musulmai; ku zabi wanda ku ke ganin ya fi dacewa.

Kara karanta wannan

2023: PDP ta yanke shawarar tsayar da dan takarar shugaban kasa daga arewa – Babangida Aliyu

“Idan ba ku dauki wannan a matsayin alhaki ne da ke daure a kan ku ba, kun ci amanar musulunci. Wajibi ne ku samo hadin kan kasa don tabbatar da kwanciyar hankali, ilimi da hadin kai.”

A bangaren gwamna Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da adalci ga kowa ba tare da kallon addini ko al’ada ba.

Bello ya kara da cewa, ya gano sabbin salon zaman lafiya, so, jajircewa da sauransu a taron.

Khalifan Tijjaniyya na duniya da sauran manya sun wuce taron Zikirin da SLS ya shirya, sunki zuwa na Ganduje

A wani labari na daban, Khalifan Tijjaniyya na duniya, Sheikh Mahy Niasse da sauran manyan shugabannin Tijjaniyya sun ki zuwa taron zikiri wanda gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shirya a fadar sarkin Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Zikiri taro ne wanda malamai sufaye su ke yi don addu’o’i, kuma ana sa ran za ayi shi ne a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

Majiyoyi sun ce taron na Kano ya zo rana daya da wani zikiri na Lokoja wanda sabon shugaban darikar Tijjaniyyar na Najeriya kuma tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel