Shugaba Buhari ya tura tawaga Kano don gaisuwar ta'aziyyar Dr Ahmad BUK

Shugaba Buhari ya tura tawaga Kano don gaisuwar ta'aziyyar Dr Ahmad BUK

  • Tawagar gwamnatin tarayya ta dira jihar Kano don gaisuwar ta'aziyyar rashin Sheikh Ahmad Ibrahim Bamba
  • Babban Malamin ya rasu ne ranar Juma'a bayan rashin lafiya da yayi gajeruwa
  • Daruruwan mutane sun halarci Sallar Jana'iza tare da birne babban malamin

Kano - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura tawaga ta musamman jihar Kano domin ta'aziyyar rashin Shehin Malamin addini, Dr Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba.

Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya jagoranci tawagar zuwa birnin Kano ranar Asabar, 8 ga watan Junairu, 2022.

Tawagar ta hada Ministan Labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, da mai magana da yawun Shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

Daily Trust ta ruwaito cewa sun dira Masallacin ne misalin kare 4 na la'asar.

Shugaba Buhari ya tura tawaga Kano don gaisuwar ta'aziyyar Dr Ahmad BUK
Shugaba Buhari ya tura tawaga Kano don gaisuwar ta'aziyyar Dr Ahmad BUK Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malam Garba Shehu ya bayyanawa iyalan mamacin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya turosu ne domin jajantawa musu da al'ummar Kano gaba daya.

Malam Pantami tace mutuwar Malamin babban rashi ne ga al'umma kuma ya bar gibi mai fadi.

Wanda ya karbi bakuncinsu, Limamin jami'ar BUK, Dr Abubakar Jibrin, ya godewa Shugaban kasa da tawagar bisa gaisuwar da suka kawo.

Rasuwar babban Malamin addini, Dr Ahmad BUK

Dakta Ahmad Muhammad Bamba wanda aka fi sani da Dr Ahmad BUK ya rigamu gidan gaskiya.

Legit Hausa ta tattaro cewa Malamin ya rasu ne da safiyar Juma'a, 4 ga watan Jumada Thani wanda yayi daidai da 7 ga watan Junairu, 2022.

An gudanar da Jana'iza Da Karfe 1:30 Na Rana a Darul Hadith Tudun Yola, Kano bayan Sallar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel