Da duminsa: Allah ya yiwa babban Malamin addini, Dr Ahmad BUK, rasuwa

Da duminsa: Allah ya yiwa babban Malamin addini, Dr Ahmad BUK, rasuwa

  • Daya daga cikin manyan Malaman Hadisi a Najeriya, Sheikh Ahmad Bamba ya rasu
  • Dalibansa sun sanar da cewa za'ayi jana'izarsa bayan Sallar Juma'a a jihar Kano
  • Malamin ya rasu yana dan shekara 82 a duniya

Kano - Babban Malamin addini mai wa'azi, Dakta Ahmad Muhammad Bamba wanda aka fi sani da Dr Ahmad BUK ya rigamu gidan gaskiya.

Legit Hausa ta tattaro cewa Malamin ya rasu ne da safiyar Juma'a, 4 ga watan Jumada Thani wanda yayi daidai da 7 ga watan Junairu, 2022.

Za'a gudanar da Jana'iza Da Karfe 1:30 Na Rana a Darul Hadith Tudun Yola, Kano bayan Sallar Juma'a, daliban Malamin suka bayyana a shafin karatunsa na Facebook.

Suka ce:

"Innah lillahi wa Innah ilaihir raji'un
A Yau Juma'a Allah ta'ala ya yiwa malamin mu Dr Ahmad muhammad ibrahim Darul Hadith Rasuwa

Kara karanta wannan

Bayan wata da watanni ana rigingumu, Mai Mala Buni ya sasanta rikicin APC a Gombe

Za'ayi Janaza a kofar gidan sa Masallacin Darul Hadith Tudun Yola kano Karfe 1:30pm"

Da duminsa: Allah ya yiwa babban Malamin addini, Dr Ahmad BUK, rasuwa
Da duminsa: Allah ya yiwa babban Malamin addini, Dr Ahmad BUK, rasuwa
Asali: Facebook

Malamai, daliban ilimi da mutane sun yi alhini da addu'ar Allah ya jikansa:

Dr Omar Disina yace:

"Mutuwar Malami Babbar Musifa ce
Innalillahi wainna ilaihi Rajioon!!
Allah ka jikan Dr Ahmad Ibrahim Bamba Kano!!
Allah ya kai haske kabarinka kamar yadda ka haska zukatan Mutane da hasken Hadisai!!!"

Dr Kabir Asgar:

"Mutuwa Rigar Kowa
Mutuwar malamai tana daga cikin babbar jarawabar da Allah ke yi wa bayinsa
Allah Ubangiji ya gafarta wa Dr Ahmad Ibrahim BUK
Allah ya sa mutuwa hutu ne
Allah ya sa aljanna ce makomarsa"

Sheikh Yusuf Musa Asadus-Sunnah:

"Allah yayima Babban Malamin Addinin musulunci Sheikh Dr Ahmad BUK Kano Rasuwa Yanzu."

Audu Bulama Bukarti yace:

Kara karanta wannan

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un: Fitaccen Shehin Tijjaniyya a Najeriya ya rigamu gidan gaskiya

"Allahu Akbar! Allah Ya gafarta wa Shaykh Ahmad Bamba (Kala Haddasana), Ya sa aljanna ce Makomarsa. Allah Ya kyauta Makwanci, Ya kyauta ta mu bayan ta su."

Dr. Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo:

"Allah ya jikan malaminmu Dr Ahmad B. U. K. Ya yi masa rahama, ya sa ya huta, ya ba shi Aljanna Madaukakiya. Ameen"

Asali: Legit.ng

Online view pixel