Karin bayani: Wata mota ta kama da wuta a kan gadar Mainland ta jihar Legas

Karin bayani: Wata mota ta kama da wuta a kan gadar Mainland ta jihar Legas

  • Yanzun nan wata mota ta kama da wuta a wani yankin jihar Legas, lamarin da ya kai konewar kayan da ta dauko
  • Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, jami'an kashe gobara basu zo ba, sannan ba a san adadin barnar da gobarar ta jawo ba
  • Wannan lamari ya faru ne a kan gadar Third Mainland da ke Legas, daya daga cikin manyan gadoji a Afrika

Legas - Wata mota kirar bas dauke da buhunna a halin yanzu tana cin wuta a karshen gadar Third Mainland a jihar Legas.

Bidiyon faruwar lamarin da Legit.ng ta gani ya nuna wani kaso mai yawa na motar bas din da tuni ya kama da wuta wanda hakan ya sa ababen hawan da ke zuwa su ci gaba da bin hanyoyin da ke nesa da wajen saboda tsananin hayaki da zafi da take tashi.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da direban mota tare da fasinjoji 4 a Abuja

Gobara a jihar Legas
Yanzu-Yanzu: Wata mota ta kama da wuta a gadar Mainland tan jihar Legas | Hoto: Wale Alameen
Asali: UGC

Gobarar ta janyo cunkoson ababen hawa a gefen gadar da ke kusa da karhsne Oworonshoki wanda ya hada da babban titin Apapa-Oshodi da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Duk da cewa ba a iya gano musabbabin barkewar gobarar ba, da alama tartsatsin wuta ne ya tashi ya kame abubuwan da ke cikin buhunan har ya zama gobara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a ga motocin kashe goba a wurin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Game da Gadar Third Mainland

Gadar Third Mainland tana daya daga cikin muhimman yankuna da suka hada tsibirin Legas a karshen jihar zuwa yankin Mainland.

Gadar mai nisan kilomita 11.8 an ruwaito ita ce mafi tsayi a cikin gadoji uku da suka hada gadar Legas Island da Mainland.

Gadar ta taso ne daga Oworoshoki kuma ta tsaya a mahadar Adeniji Adele da ke tsibirin Lagos Island.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Wasu masu tone kabari su sace sassan jikin mamata sun shiga hannu

Ana daukar gadar a matsayin gada mafi tsawo a Afirka har zuwa shekarar 1996 lokacin da aka fara amfani da gadar Oktoba 6 a Alkahira.

A wani labarin, mummunar gobarar tsakar dare ta lakume kayan miliyoyin naira a fitacciyar kasuwar Ladipo ta siyar da kayayyakin kayan gyara ta Legas.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an gano cewa gobarar ta fara ne daga wani shagon kafintoci da ke kan titin Ladipo amma daga bisani ta karasa har wata ma'adanar kayan gyaran Toyota da ke da kusanci da wurin.

Majiyoyi sun ce gobarar ta fara ne sakamakon tartsatsin da wutar lantarki ta yi a shagon kafintocin amma daga bisani ta kai har shago mai lamba 85, Ladipo Street by Fatai Atere way, Ladipo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel