Tirkashi: Ledar Fiyo wota 1 ya tashi daga N10 ya koma N20 a jihar Kogi
- Kungiyar masu hada ruwan sha na leda, reshen jihar Kogi ta bayar da sanarwa akan kara farashin kudin ko wacce ledar fiyo wota inda zai tashi daga N10 zuwa N20
- A cewar kungiyar, hakan ya na da alaka da tashin farashin abubuwan da ake amfani da su wurin hada ruwar wanda ya ke da alaka da tashin farashin Dala
- Dama tun shekarar da ta gabata kungiyar ta dage farashin jakar fiyo wota daga N100 zuwa N130 sakamakon tabarbarewar tattalin arziki saboda COVID-19
Kogi - Kungiyar masu hada ruwan sha na leda, reshen jihar Kogi sun bayyana kudirinsu na dage farashin ruwan leda wanda aka fi sani da fiyo wata daga N10 zuwa N20.
Kungiyar ta ce hakan yana da alaka da yadda farashin abubuwa su ka tashi bisa tashin farashin dala, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: UGC
Daily Trust ta gano yadda kungiyar ta daga farashin ruwa a shekarar da ta gabata inda jaka daya ta koma N130 daga N100 bayan tabarbarewar tattalin arziki saboda annobar COVID-19.
Shugaban kungiyar, Mr Joseph Eseyin, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da su ka yi da Daily Trust a Lokoja, babban birnin jihar a ranar Laraba.
Ya ce kowacce jakar ruwa za ta koma N200 saboda halin tabarbarewar tattalin arzikin kasa.
Ya kara da cewa, ba su yi hakan don cutar da jama’a ba sai dai don tallafa wa masu hada ruwan wurin samun damar siyan ababen hada ruwan da tace su don su dace da NAFDAC.
Eseyin ya ce yanzu litar man fetur ta karu zuwa N165 kuma yanzu haka jakunkunan ledoji da ake zuba ruwan sun koma N1.6m ko wacce tonne kuma ko wanne bandir yanzu N7,000 yake, har kudin diesel ma ya daga.
Ya kara da cewa, sabon farashin ruwan zai koma N20 a fadin jihar. Kuma ya roki masu harkar sayar da ruwa da su bayar da hadin kai wurin bin sabon farashin ruwan.
Eseyin ya ce ATWAP ya ce za su yi kwalema ta kwana uku don samun damar gamsar da ma’abota amfani da ruwan iyakar iyawar su.
Buhari: Na san baƙar uƙuba da tsabar wahalar da ƴan Najeriya ke ciki
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya ce ya na sane da bakar ukuba da kuma tsabar wahalar da 'yan Najeriya suke shiga kafin su ciyar da kansu da iyalansu a karkashin mulkinsa.
Shugaban kasan wanda ya sanar da hakan yayin da ake zantawa da shi a gidan talabijin na Channels, ya kara wa mutane karfin guiwa da su duba noma da kiwo a matsayin mafita.
Shugaban kasan wanda ya sanar da hakan yayin da ake zantawa da shi a gidan talabijin na Channels, ya kara wa mutane karfin guiwa da su duba noma da kiwo a matsayin mafita.
Asali: Legit.ng