Buhari: Na san baƙar uƙuba da tsabar wahalar da ƴan Najeriya ke ciki

Buhari: Na san baƙar uƙuba da tsabar wahalar da ƴan Najeriya ke ciki

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa yana sane da halin ukuba da tsabar wahala da 'yan Najeriya suke ciki karkashin mulkinsa
  • A cewarsa, a sane ya ke da halin da 'yan Najeriya suke shiga kafin su ciyar da kansu tare da iyalansu a kasar nan karkasin mulkinsa
  • Sai dai ya shawarci 'yan Najeriya da su hanzarta komawa noma, ya ce duk da yawan 'yan kasar, kashi 2.5 na kasar kacal ake nomawa a kasar nan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya ce ya na sane da bakar ukuba da kuma tsabar wahalar da 'yan Najeriya suke shiga kafin su ciyar da kansu da iyalansu a karkashin mulkinsa.

Shugaban kasan wanda ya sanar da hakan yayin da ake zantawa da shi a gidan talabijin na Channels, ya kara wa mutane karfin guiwa da su duba noma da kiwo a matsayin mafita.

"Tabbas na san wahalar da mutane suke ciki," yace. "Amma kamar yadda nace, ku kalla yawan 'yan Najeriya, kashi 2.5 na kasa ne ake nomawa.
Buhari: Na san baƙar uƙuba da tsabar wahalar da ƴan Najeriya ke ciki
Buhari: Na san baƙar uƙuba da tsabar wahalar da ƴan Najeriya ke ciki. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC
"A gaskiya mun gano hakan yayin da lokaci ya kure, amma ya zama dole mu koma gona."

A yayin tattaunawar, shugaban kasa Buhari ya yi magana kan wasu matsalolin da suka dade suna ci wa kasar nan tuwo a kwarya da suka hada da tsaro, tattalin arziki, siyasa da sauransu.

Kamar yadda ChannelsTV ta ruwaito, ya yaba wa kokarin mulkinsa tunda ya hau kujerar shugabacin kasa a shekarar 2015, ballantana a manyan fannonin tsaro, inganta tattalin arziki da kuma yaki da rashawa.

Shugaban kasan ya yarda cewa abubuwa sun cigaba kuma mulkinsa na cigaba da inganta tattalin arziki duk da halin da kasar nan ke ciki.

Ba zan saki Nnamdi Kanu ba, ya kare kan shi a gaban kotu, Buhari

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, ya gurfana a gaban kotu tare da kare kansa a kan labaran karya da ya dinga yadawa a kasashen ketare kan mulkinsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban dan a waren IPOB, Nnamdi Kanu, ya kare kansa gaban kotu akan yada karairayi dangane da mulkinsa lokacin ya na kasashen ketare.

Buhari ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa wacce gidan talabijin din Channels ta nuna a ranar Laraba kuma Legit.ng ta kula da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel