Hedkwatar tsaro ta ja kunnen ‘yan siyasa da sauran jama’a kan amfani da kayan sojoji

Hedkwatar tsaro ta ja kunnen ‘yan siyasa da sauran jama’a kan amfani da kayan sojoji

  • Hedkwatar tsaro ta ja kunne akan bayyanar fostocin wasu ‘yan siyasa da wasu fararen huluna sanye da kayan sojojin su na kamfen a jihohinsu
  • Mukaddashin darektan labaran soji, Wap Maigida ya saki wata takarda yana jan kunne akan hakan a ranar Alhamis a Abuja
  • Maigida ya ce hakan cin mutunci ne za su dauki mataki a kai don sojoji ba su da wata alaka da siyasa ko kuma harkokin farar hula

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta Najeriya (DHQ) ta ja kunne akan yadda ‘yan siyasa su ke yin fostocin kamfen sanye da sutturun sojoji, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mukaddashin darektan labaran sojoji, Wap Maigida ya ja kunne akan yin hakan ta wata takarda da ya saki ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai yin ka: El-Rufai ya sanar da mataki 1 tak na magance 'yan bindiga

Hedkwatar tsaro ta ja kunnen ‘yan siyasa da sauran jama’a kan amfani kayan sojoji
DHQ ta gargadi 'yan siyasa da sauran al'umma kan amfani da kayan sojoji. Hoto: DHQ
Asali: Facebook

Mr Maigida, wanda sojan sama ne ya ce fostocin kamfen din wasu gwamnoni sun bayyana sanye da kayan sojoji a fitattun wurare a jihohinsu.

Hakan cin mutuncin soji ne

A cewarsa hakan bai dace ba kuma cin mutunci ne farar hula su dinga sa kayan sojoji yayin horarwa irin na sojoji.

Kamar Premium Times ta bayyana ya ja kunne a cikin takardar inda yace:

“Wajibi ne girmama dakarun sojin Najeriya a matsayin cibiya ta musamman wacce ba ta da dangantaka da siyasa ko makamancin hakan, kuma ba ta bukatar a sa ta cikin harkar siyasa.
“Don haka ya kamata a shawarci ‘yan siyasa da wasun su da su guji amfani da kayan sojoji don yin harkokin siyasa da sauransu.”

Ya ce za a fara daukar mataki

Kara karanta wannan

An rasa sojoji 6, 'yan Boko Haram 22 sun sheka barzahu bayan luguden da MNJTF suka yi a Borno

Ya kara da cewa:

“Abin kula a nan shi ne, duk wanda aka kama da laifin sake yin hakan, za a daure iya shi.”

Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep

A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.

A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.

Asali: Legit.ng

Online view pixel