An rasa sojoji 6, 'yan Boko Haram 22 sun sheka barzahu bayan luguden da MNJTF suka yi a Borno

An rasa sojoji 6, 'yan Boko Haram 22 sun sheka barzahu bayan luguden da MNJTF suka yi a Borno

  • Sojojin hadin guiwa na kasa da kasa shida sun rasa rayukansu a luguden wutan da suka yi kan 'yan Boko Haram a Mallam Fatori a jihar Borno
  • Hukumomi sun tabbatar da yadda sojojin suka yi wa 'yan Boko Haram luguden wuta inda suka halaka mayakan 22 yayin da wasu suka jigata
  • Zakakuran sojojin sun samo motocin yaki, babura, bindigogi da sauran miyagun makamai daga hannun 'yan ta'addan

Borno - Hukumomin sojojin Najeriya a ranar Alhamis sun tabbatar da mutuwar sojoji shida sakamakon arangamar dakarun sojin hadin guiwa na kasa da kasa da 'yan Boko Haram a garin Mallam Fatori kusa da tafkin Chadi.

Channels TV ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan ba su tafi haka ba, an halaka 22 daga cikin su.

Kara karanta wannan

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

An rasa sojoji 6, 'yan Boko Haram 22 sun sheka barzahu bayan luguden da MNJTF suka yi a Borno
An rasa sojoji 6, 'yan Boko Haram 22 sun sheka barzahu bayan luguden da MNJTF suka yi a Borno. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wata takarda da mai magana da MNJTF ta fitar, Kanal Muhammad Dole, ya bayyana cewa, rundunar Sharan Fage ta na da sojoji da Monguno a Najeriya, Diffa daga Nijar kuma sun samu taimakon Operation HADIN KAI wadanda suka ragargaji 'yan Boko Haram da ke boye wa a Mallam Fatori.

Kamar yadda yace, dakarun sun hadu da gagararrun 'yan ta'adda wadanda suka kaddamar da farmaki, suka nasa abubuwa masu fashewa a hanyar da dakarun za su wuce kuma suka kai wa ababen hawansu farmaki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma kuma, dakarun sun nuna wa 'yan ta'addan fin karfi, lamarin da yasa suka tsere tare da barin maboyarsu.

A yayin musayar wutan, Kanal Dole ya ce 'yan Boko Haram 22 ne aka halaka yayin ruwan wutar, yayin da aka kwace motocin yaki 5, babura 5 da bindigogi takwas da sauransu.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Kwamandan ISWAP, Abou Maryam, ya sheka barzahu sakamakon luguden sojin NAF

Abun takaici in ji Kanal Dole, an rasa rayukan jami'ai 6 na MNJTF yayin da wasu 16 suka samu miyagun raunika.

Ya kara da bayyana cewa, mutum 17 aka kama wadanda ake zargi a yankin, Channels TV ta ruwaito.

Nasrun Minallah: Kwamandan ISWAP, Abou Maryam, ya sheka barzahu sakamakon luguden sojin NAF

A wani labari na daban, Dakarun sojin Najeriya sun halaka kwamandan kungiyar ta'addanci ta ISWAP, Modu Kime, wanda aka fi sani da Abou Maryam da mayakansa a wani luguden ruwan wuta da aka yi musu wuraren tafkin Chadi da ke jihar Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa, manyan kwamandojin kungiyar ta'addancin sun hadu da ajalinsu ne yayin da aka kai musu farmaki wuraren rafikan Bisko da Tumbum da ke karamar hukumar Abadam ta jihar.

An aiwatar da samamen ne bayan sintirin jiragen sama da kuma bayanan sirri da suka nuna cewa shugabannin ta'addancin suna wurin.

Kara karanta wannan

Bayan farmakin ISWAP a Borno, Buhari yace ana matakin karshe na yaki da 'yan ta'adda

Asali: Legit.ng

Online view pixel