An fara shirin kara farashin fetur, Osinbajo zai zauna da NLC a kan batun biyan N5,000

An fara shirin kara farashin fetur, Osinbajo zai zauna da NLC a kan batun biyan N5,000

  • Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki tace babu ja da baya kan batun cire tallafin fetur
  • Zainab Ahmed tace za a duba tsare-tsaren da za a shigo da su idan an daina biyan tallafin fetur a Najeriya
  • Farfesa Yemi Osinbajo zai shugabanci wani kwamiti da zai tattauna da wakilan NLC domin a samu mafita

Abuja - Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya da gaske take yi a kan batun janye tallafin fetur.

Jaridar Punch ta rahoto Zainab Ahmed ta na cewa Mai girma Farfesa Yemi Osinbajo zai jagoranci zaman da za ayi da kungiyar ‘yan kwadago a kan lamarin.

Mataimakin shugaban kasar zai jagoranci tattaunawar da gwamnati za tayi da NLC da masu ruwa da tsaki da nufin rage radadin da jama’a za su shiga.

Kara karanta wannan

Ba za ta yiwu a tsaida Musulmi da Musulmi takara ba, sama da kasa za su hade inji CAN

Gwamnatin tarayya ta na tunanin rabawa marasa karfi N5, 000 da kuma shigo da wasu dabarun da za su sa cire tallafin man fetur din ba zai yi tasiri sosai ba.

Akwai aiki a gaban Osinbajo

Kwamitin Yemi Osinbajo aka ba alhakin shawo kan ‘yan kungiyar kwadago wanda ba su goyon bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ta kara farashin mai.

Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: HARUSPICE
Asali: Facebook

Ahmed tace kwamitin zai duba abin da ya fi dacewa ayi wa marasa hali bayan an dawo hutun sabuwar shekara, inda za a ji ta bakin NLC da sauran jama’a.

Dole fetur zai tashi - Minista

Da take amsa tambayoyin ‘yan jarida, an rahoto Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin ta na cewa gwamnati za ta cire hannunta a kan fetur.

Kara karanta wannan

An ci gaba da shagalin biki bayan an sako amaryar da aka sace a Filato

Zainab Ahmed tace kasafin kudin shekarar bana ya yi aiki da dokar Petroleum Industry Act 2021.

Game da batun rabawa talakawa N5, 000 domin su samu kudin zirga-zirga, Ahmed tace har yanzu ana duba yiwuwar yin hakan ne, ba a tabbatar da tsarin ba.

Baya ga maganar raba kudin, Ministar tattalin arzikin tace akwai wasu dabaru da gwamnati ta ke dubawa domin ganin tashin mai bai taba maras karfi sosai ba.

An ba masu nakasa aiki

A yau ne aka ji yadda Uwargidar shugaban kasa ta shiga-ta fita har aka ba wasu matasa masu nakasa aiki a gwamnatin tarayya bayan sun kammala NYSC.

Darekta Janar na NYSC, Shuaib Ibrahim yace Aisha Muhammadu Buhari ta nemawa matasan biyu aiki a hukumar Nigeria Social Insurance Trust Fund (NSITF).

Asali: Legit.ng

Online view pixel