Mai dakin Buhari ta canza masu rayuwa, tayi wa masu nakasa hanyar samun aiki mai-tsoka

Mai dakin Buhari ta canza masu rayuwa, tayi wa masu nakasa hanyar samun aiki mai-tsoka

  • Uwargidar shugaban kasa ta shiga-ta fita har aka ba wasu matasa masu nakasa aiki a gwamnatin tarayya
  • Aisha Muhammadu Buhari ta nemawa matasa biyu aiki a hukumar Nigeria Social Insurance Trust Fund (NSITF)
  • Har ofishin NYSC DG aka je aka ajiye takardar samun aikin Onogberie Efe Lulu da Nuruddeen Tahir a garin Abuja

FCT, Abuja - Mai girma Aisha Muhammadu Buhari, ta sa hannu wajen samawa wasu Bayin Allah biyu da suka kammala bautar kasa watau NYSC aikin yi.

A ranar Alhamis, 6 ga watan Junairu, 2022 ne jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Aisha Muhammadu Buhari ta taimakawa wadannan mutane.

Wadannan Bayin Allah; Onogberie Efe Lulu da Nuruddeen Tahir, su na fama da nakasar halitta.

Mataimakin darektan harkokin sadarwa da yada labarai na hukumar NYSC, Emeka Mgbemena, ya bayyana wannan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya nada sabbin jami'ai na hukumar gudunarwa ta NNPC

Emeka Mgbemena yace uwargidar shugaban Najeriyar ta taimakawa wadannan mutane masu fama da nakasa ne saboda kiran DG, Janar Shuaibu Ibrahim.

Birgediya Janar Ibrahim ya dade ya na kira na musamman cewa a rika duba walwalar masu bautar kasa, wanda a karshe irin hakan ya ceci Lulu da Tahir.

Sun samu aiki
Onogberie Efe Lulu da Nuruddeen Tahir Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

Za su yi aiki a hukumar NSITF

Kamar yadda sanarwar NYSC ta bayyana, Onogberie Efe Lulu da Nuruddeen Tahir sun samu aiki ne a hukumar nan ta Nigeria Social Insurance Trust Fund.

Har ofishin Darekta Janar na NYSC na kasa aka je aka kai takardun bada aikin Efe Lulu da Tahir wanda ba su dade da kammala aikin yi wa kasa hidima ba.

An yi wa Aisha Buhari godiya

A jawabin da ya fitar, PR Nigeria tace Birgediya Janar Ibrahim ya godewa Aisha Buhari saboda irin kokarin da tayi wajen neman canza rayuwar matasan biyu.

Kara karanta wannan

Dawo-dawo: Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya yi zaman sirri da masu so ya koma kan mulki

Janar Ibrahim yace wannan taimako da uwargidar shugaban Najeriyar tayi zai karawa masu fama da nakasa kwarin gwiwa, su ji cewa an san da zaman su.

Lulu da Nuruddeen sun godewa Aisha Buhari da wannan alheri, tare da rokon Ubangiji ya saka mata.

Na san ana ji a jika - Buhari

A ranar Laraba ne aka ji Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana sane da irin bakar ukuba da kuma tsabar wahalar da 'yan Najeriya suke shiga a halin yanzu.

Da aka yi hira da shi, Mai girma Muhammadu Buhari ya yi kira ga mutane su rungumi nowa da kiwo domin samun mafita daga halin kangin da ake ciki a mulkin na sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel