Farashin Coca Cola, Fanta, dss zasu tashi yayinda Gwamnati kara haraji N10 kan litan lemun kwalba

Farashin Coca Cola, Fanta, dss zasu tashi yayinda Gwamnati kara haraji N10 kan litan lemun kwalba

  • Ministar Kudi ta bayyana sabon kudin haraji kan lemun kwalba don mutane su daina sha
  • Zainab Shamsuna Ahmed ta ce ana son yan Najeriya su daina shan lemun kwalba sabon suna haifar da ciwon Siga
  • Hakazalka wannan zai taimaka wajen samar da kudin shiga

Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da karin kudin harajin N10 ga litan dukkan lemukan kwalba marasa bugarwa.

Ministar Kudi, Kasafin Kudi, da shirye-shiryen tarayya, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa an yi wannan kari ne don hana mutane shan kayan kwalba irinsu Coca-Cola, Pepsi, Sprite, dss saboda yawaitan cututukan dake da alaka da Siga irinsu kiba da ciwon siga.

A cewar rahotanni, sama da yan Najeriya milyan hudu ke fama da ciwon Siga sakamakon yawan shan kayan zaki.

Farashin Coca Cola, Fanta zasu tashi
Farashin Coca Cola, Fanta, dss zasu tashi yayinda Gwamnati kara haraji N10 kan litan lemun kwalba Hoto: Thecable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ku yiwa 'yayanku tarbiyya bisa al'adunmu, Lai Mohammed ya yi kira ga iyaye

Ministar ta bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja yayinda bayani kan kasafin kudin 2022 da Shugaba Buhari ya rattafa hannu, rahoton Leadership.

Ta bayyana cewa wannan kari na kunshe cikn dokar kudi ta 2021.

Gwamnati ta ce wannan kari zai taimaka wajen samar da karin kudin shiga domin yin ayyuka da dama.

A riwayar TheCable, tace:

"Yanzu akwai harajin N10/lita kan dukkan kayan kwalba maras sa maye. An yi hakan ne don kawar da hankulan mutane daga shan wadannan kayan Sigan da suke bada gudunmuwa wajen ciwon siga da kiba."
"Kuma hakan zai taimaka wajen samar da kudin shiga don kashewa sashen kiwon lafiya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel