Yanzu-yanzu: Tun hawa mulki, Shugaba Buhari ya nada mai bashi shawara kan tattalin arziki na farko

Yanzu-yanzu: Tun hawa mulki, Shugaba Buhari ya nada mai bashi shawara kan tattalin arziki na farko

Bayan shekaru shida da rabi kan karagar mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada mutum daya matsayin mai bashi shawara kan harkokin tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban kasan ya nada Dr Doyin Salami a ranar Talata, 4 ga wata, 2021.

Mai magana da yawun Shugaban, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook.

Yace:

"An nada babban mai baiwa Shugaban kasa shawara kan tattalin arziki. Shine Dr Doyin Salami, wanda ya kasance Shugaban kwamitin bada shawara kan tattalin arziki."
Yanzu-yanzu: Tun hawa mulki, Shugaba Buhari ya nada mai bashi shawara kan tattalin arziki na farko
Yanzu-yanzu: Tun hawa mulki, Shugaba Buhari ya nada mai bashi shawara kan tattalin arziki na farko
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa Dr Doyin Salami ya kammala Digirinsa na Doktora a ilmin tattalin arziki a jami'ar Landan kuma shine Shugaban KAINOS Edge Consulting Limited.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Kano ya bayyana mutum daya rak da ya cancanci darewa kujerar Buhari a 2023

Wasu irin shawari zai baiwa Shugaban kasa?

Femi Adesina ya lissafa jerin shawarin da ake sa ran zai rika baiwa Shugaban kasa.

A cewarsa:

"Zai lura da lamuran tattalin arzikin kasa kuma ya baiwa Shugaban kasa shawara kansu; zai rika lura da abubuwan dake faruwa a duniya kuma ya fadawa Shugaban kasa matakin da zai dauka domin inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi, kawar da talauci, dss."

Asali: Legit.ng

Online view pixel