Gaskiyar yadda muka kubuta daga hannun kasurgumin dan bindiga Turji, Ibrahim

Gaskiyar yadda muka kubuta daga hannun kasurgumin dan bindiga Turji, Ibrahim

  • Daya daga cikin mutanen da suka kubuta daga sansanin Bello Turji, ya bayyana yadda rayuwarsu ta kasance a tare da yan bindiga
  • Ibrahim Rowa yace yana tsaka da kokarin kwashe gyaɗa da ya noma a gonarsa wasu yan bindiga suka sace shi, kwanaki 23 kenan
  • Yace ba zato ba tsammani yan bindiga suka bude su kuma suka haɗa su da yara waɗan da suka nuna musu hanya

Zamfara - Ɗaya daga cikin mutane sama da 50 da suka kubuta daga hannun ɗan bindiga Bello Turji, ya bayyana yanayin da suka shiga a sansanin yan ta'addan, kamar yadda Channels Tv ta rahoto.

Bello Turji, ya yi kaurin suna wajen aikata ayyukan ta'addanci da suka haɗa da kashe mutane da garkuwa a yankunan Shinkafi, Sabon Birni, Isa a Zamfara da Sokoto.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Zariya, sun kashe mutane

Mutumin mai suna Ibrahim Bakada Rowa, da sauran mutane sun kubuta ne bayan luguden wutan sojoji a sansanonin yan bindiga dake kusa da inda suke a dazukan Zamfara da Sokoto.

Ibrahim Rowa
Gaskiyar yadda muka kubuta daga hannun kasurgumin dan bindiga Turji, Ibrahim Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shin yan bindigan na azabtar da su?

Da yake zantawa da manema labarai bayan kubutarsa, Rowa yace ya kwashe kwanaki 23 a hannun yan bindiga bayan sace shi a gonarsa yana aiki.

Yayin da yake a sansanin Turji, yace yan bindigan suna girka musu shinkafa, kuma suna ba su abinci da ruwa kowace rana.

Ya nuna tsantsar farin cikinsa da samun yanci ranar Talata, yace:

"Ina matukar farin ciki da murna a yau da kasancewa cikin waɗan da suka kubuta. Ina cikin haƙo gyaɗa a gona ta aka sace ni, na kwashe kwanaki 23 kenan a hannun su ba tare da an bani ko sisi ba."

Kara karanta wannan

'Yan sanda: Yadda muka ceto mata masu juna biyu 7 daga hannun Turji a Zamfara

Ta ya kuƙa samu yanci?

A cewar Malam Ibrahim ba zato suka umarci ya fito daga ɗakin da suke tsare kuma suka ba shi makullai ya bude sauran.

"Muna zaune mu 8 a ɗakin da ake tsare da mu lokacin da suka umarci mu fito. Yan bindigan suka bani makullai domin na bude sauran mutanen da suka sato."
"Bayan mun fito mun jeru, sai suka haɗa mu da kananan yara, waɗan da suka zame mana jagora zuwa kan hanya."

A wani labarin na daban kuma Bayan cikar watanni uku, Gwamna El-Rufa'i ya kara wa'adin hana Acaba a jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta kara wa'adin hana Okada, yawo da makami da sauran matakan da ta ɗauka har sai baba ta gani

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida, Samuel Aruwan, yace matakan na nan daram har sai gwamnati ta fitar da sanarwa kan matakan nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel